Dalia Hernández

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dalia Hernández
Rayuwa
Haihuwa Veracruz (en) Fassara, 14 ga Augusta, 1985 (38 shekaru)
ƙasa Mexico
Karatu
Makaranta Universidad Veracruzana (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo da dan wasan kwaikwayon talabijin
IMDb nm2199664

Dalia Hernández Armenta (an haifeta ranar 14 ga watan Agusta, 1985) ƴar wasan kwaikwayo ce, ta ƙasar Meziko, wadda aka haifa a Veracruz, Mexico.[1] An santa saboda irin rawar ganin da ta taka a cikin fim ɗin Apocalypto (2006),[2] da The Legend of the Maska (2014) da kuma, Miracle Underground (2016).

A cikin shekarar 2007, ta lashe lambar yabo ta Imagen Award don mafi kyawun goyon bayan ƴar wasan kwaikwayo, duba da rawar da ta taka a fim ɗin Apocalypto.[3] Ya taka rawa a cikin jerin shirin TV masu dogon Zango; "Capadocia del 2008" a cikin kashi na "María Magdalena" inda ya fito a matsayin "Rosa". A cikin 2014 ta taka rawar "Nayeli" a cikin The Legend of the Maska kuma a matsayin "Patricia" a cikin fim ɗin Miracle Underground.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Dalia Hernandez". CINeol (in Sifaniyanci). Retrieved 21 January 2016.
  2. "Best Movies of 2006". Lassen County Times. 16 January 2007. Retrieved 21 January 2016.
  3. "'Ugly Betty' Wins at 22nd Imagen Awards". AP Online. 29 July 2007. Archived from the original on 20 February 2016. Retrieved 21 January 2016 – via HighBeam Research.