Dambu
| Dambu | |
|---|---|
|
| |
| Kayan haɗi | Masara |
| Kayan haɗi |
Zogale, cooking oil (en) |
| Tarihi | |
| Asali | Nijar da Najeriya |
|
|
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
|


Dambu, wani kalan abinci ne wanda ya samo asali a ƙasar Hausawa a tarihi. Dambu abinci ne daba ko wacce mace ta iya yin shi ba, hasali ma ko da mace ta ƙware wajen yin danbu, to fa wata rana sai ya ba da ita (sai yabadda itta a wani ɓangaren) ya kan iya shaƙe mutum musamman idan ana cin shi babu ruwa a kusa.
Dambu yana da farin jini a wurinmutanai har ma da samari da ƴan mata idan su kayi marmarin shi.
Ya kan haifar da ƙoshi nan da nan idan aka sanya mishi haɗin ƙuli-ƙuli ko yaji.

Dambu Abincin Hausawa ne da ake yin shi da tsakin masara ko Shinkafa da Rama ko Yakuwa koTafasa ko zogale ko kabeji, ana dafawa ne ta hanyar yin Siraci(tirare).
Rabe-raben dambu
Shi dai dambu ya kasu kashi-kashi akwai dambun tsakin masara akwai kuma na dambun Shinkafa amma wanda. Yafi tasiri a gargajiyan ce shi ne dambun tsakin masara wanda mafi yawan mutanen Najeriya suna cin shi musamman ɗan Arewa.[1][2]
Dambu yana da nau'i biyu
[gyara sashe | gyara masomin]Dambun tsakin masara
Dambun ɓarjajjiyar Shinkafa.
Dambun ɓarjajjiyar alkama
Har dambun garin masara ana yi yanzu. Wasu mutane su kan ci shi da mai da yaji, wasu su ci shi da miyan dage-dage.
Kayan yin dambu
[gyara sashe | gyara masomin]A na yin Dambu da tsaki (ɓarjin inji wanda yake da laushi amma ba sosai ba) ko na masara, ko dawa, gero,har ma dana Shinkafa.
Yadda ake yin dambu
[gyara sashe | gyara masomin]Dambu idan ka samu tsaki wanda aka ɓarza, da tafasa ko ganyen zogale,ko ganye Alaiyaho,ko kuma wani nau'in ganye da muke amfani da shi, ka samu ruwa, gishiri Maggi.sai ka ɗora tukunyar ƙarfe a wuta ko ainahin tukunyar yin dambun sai ka saka ruwan ba mai yawa ba, daga nan sai ka kawo tukunya ta ƙasa wadda a ƙasanta fasasshe ne sai a dora ta a wannan tukunyar ƙarfe da aka sa ruwa sai a kwaɓa wani abun ɗorawa, ko toka ko kuma duk wani abunda za'a iya amfani dashi don like tukunya biyu. Bayan ka liƙe su sai ka samu wani dan murfi wanda zai shiga cikin bakin tukunya ƙasa dinnan tunda daman nache za'a fasa kasan tunkunya, sai ka sa wannan murfin yadda dai ruwan nan idan ya tafasa suracin shi zai dinga tasowa cikin tukunya kasa ɗin nan. Bayan kasa murfin sai ka zuba tsaki ka/ki da ka gyara shi ka/ki jika ba sosai ba ka sa gishiri Maggi kayan ƙamshi irin su citta kanunfari da sauransu ganyen zogale ko tafasa, sai ka sake rufewa. Bayan ya yi sai kayi fashe ka/ki zuba ruwa a fashen bayan an kwashe a roba sai a sake mayarwa cikin tukunyar sai a barshi ya dahu idan ka sauke daman ka tanadi man gyaɗa soyayye ko manja sai a zuba shi a roba ayi ta sakuma, kar a manta da ruwan sha ya kasance yana kusa, saboda yana shaƙe maƙogwaro.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://cookpad.com/ng/recipes/6141929-dambun-tsakin-masara
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html