Dan wasan tsalle-tsalle
Stephanie Ogechukwu Onusiriuka yarinya ce shahararriyar matashiyar yar wasan tsalle tsalle yar Nigeria.ƙwararriyar yar wasan wacce ke samun lambobin yabo masu yawa tun tana ƙarama. Ta lashe gasar zinare a Afirka, ta zama zakara a wasannin ƙasa, kuma gwamnati ta sanya ta cikin manyan Shahararrun yan wasa na Najeriya. Hukumar kula da wasanni da Al-adu ta Najeriya yasaka matashiyar yar wasan ne cikin manyan Shahararrun yan wasan Najeriya ne saboda gudun kar kungiyoyi daga ƙasashen ketare suyi yunƙurin ɗauke ta don haka hukumar ta bayyana cewa duk inda Yakamata take gwamnatin zata ɗauki nauyinta sannan zuwa shekarar 2026 idan tacika shekaru 16 zata fara karawa cikin gasar wasannin ƙasashe Rainon Ingila (Common Wealth)
Tarihin kwarewarta
Ta fara samun horo na musamman a Tony International Gymnastics Club(TIG)da ke Abuja, inda malamin ta mai suna Anthony Asuquo ya tabbatar da cewa tana da baiwa mai ban mamaki bayan wasu nasarori data samu y
Nasarori
A gasar ƙasa da ƙasa: Ta lashe gasar zinare ta African Gymnastics Championship a Pretoria, Afirka ta Kudu, a shekarar 2019, lokacin tanada shekaru 8 kacal .
A shekarar 2021, a National Sports Festival (Edo 2021), ta samu zinare 1, silver 2, da bronze 1 a lokacin tana da shekara 11 .
A National Youth Games (Delta 2023), ta zama mafi nasarar yan wasan gymnast a ƙasar—ta lashe zinare 4 .
Sannan, a ƙarin African Club Championships a Pretoria, ta sake lashe zinare biyu (2019 da 2022) .