Jump to content

Dark October (fim)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dark October
Dark October (fim)

Dark Oktoba fim ne na kasar Najeriya na shekarar 2023, da aka fitar a dandalin kallo na Netflix a ranar 6 ga watan fabrairu, shekarar 2023. Fim ɗin dai ya ta'allaka ne kan yadda wasu matasa huɗu da aka kashe a jami'ar Fatakwal da aka fi sani da Aluu Four lynching. An zarge mutanen huɗu ne da laifin sata a unguwar Aluu da ke Fatakwal. Fim ɗin ya tattara abubuwan da suka yi sanadiyar kashe su da kuma abin da ya biyo bayan lamarin.[1]

Ƴan wasan shirin

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Chuk Joseph
  • Munachi Okpara
  • Oriaku Kelechukwu James
  • Kem-Ajieh Ikechukwu
  • Adike Daniel
  • CO2 Jami'in
  • Oluchi Anaghara-Awa

Shiryawa da saki

[gyara sashe | gyara masomin]

Kamfanin Filmone Productions ne ke rarraba fim ɗin kuma Toka McBaror ne ya ba da Umarni. Bayan fitowar sa a Netflix a ranar 3, ga Fabrairu, 2023. Babban mai shirya fim din, Linda Ikeji ta ce tana fatan fim ɗin zai haifar da tattaunawa game da hadarin kisan gilla da kuma mahimmancin tabbatar da adalci ga kowa.[2]

Iyayen yaran da aka yi wa kaca-kaca da Aluu Four sun nuna rashin amincewa da fim ɗin kuma sun buƙaci Netflix da Linda Ikeji su dakatar da fim din tare da bayyana cewa Linda Ikeji ba ta nemi izini daga gare su ba kafin su ci gaba da yin fim game da 'ya'yansu. [3][4]

  1. "'Dark October', movie on Aluu Four lynching, set for Netflix debut". TheCable Lifestyle (in Turanci). 2023-01-15. Retrieved 2023-02-05.
  2. BellaNaija.com (2023-01-18). "Get the Scoop on Linda Ikeji's Debut Film "Dark October" Coming to Netflix February 3rd". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2023-02-05.
  3. Davies, Iheamnachor (January 25, 2023). "DARK OCTOBER: Parents of slain Aluu-4 urge Linda Ikeji, Netflix to retract movie, suspend premiere". Vanguard.
  4. Lawal, Babatunde (2023-01-26). "'Dark October': Parents of slain students call Linda Ikeji and Netflix to suspend movie premiere". Pulse Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-02-05.