Darlington Nwokocha
![]() | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2023 - 4 Nuwamba, 2023 ← Theodore Ahamefule Orji District: Abia Central
2 ga Yuni, 2022 - ← no value - Chineye Fredinard Ike (en) ![]() District: Abia Central
11 ga Yuni, 2019 - Mayu 2022 ← Chineye Fredinard Ike (en) ![]() District: Isiala Ngwa North/Isiala Ngwa South
9 ga Yuni, 2015 - ← Chineye Fredinard Ike (en) ![]() District: Isiala Ngwa North/Isiala Ngwa South | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Jihar Abiya, 1967 (57/58 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Ƙabila | Tarihin Mutanen Ibo | ||||||||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | jami'ar port harcourt | ||||||||
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Darlington Nwokocha (an haife shi 16 ga watan Agusta 1967) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya yi aiki a matsayin Sanata mai wakiltar Abia ta tsakiya daga watan Yuni zuwa watan Nuwamba 2023. [1] Kafin zaɓensa a majalisar dattawa, ya kasance ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar Isiala-Ngwa North/ Isiala-Ngwa ta Kudu daga shekarun 2015 zuwa 2019. Ya yi aiki a matsayin shugaba akan Inshora da Matsalolin Aiki a lokacin da yake Majalisa. [2] Nwokocha ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Abia daga shekarun 2007 zuwa 2015. [3] Wa’adinsa a majalisar dattawa bai daɗe ba, sakamakon soke zaɓensa da kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya ta yi. [4]
Cirewa daga Majalisar Dattawa
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023, Kotun ɗaukaka kara ta Najeriya da ke zama a Legas, ta soke nasarar zaɓen Sanata Darlington Nwokocha. [5] A baya dai ya samu nasara a wata ƙaramar kotun amma mai ƙalubalantar sa Col Austin Akobundu (mai ritaya) [6] ya ɗaukaka ƙara wanda ya kai ga cire shi daga majalisar dattawa. An maye gurbinsa da Kanar Austin Akobundu wanda ya samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara. [7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Silas, Don (27 February 2023). "Election result: INEC declares LP's Nwokocha winner of Abia Central Senatorial seat". Daily Post. Retrieved 2 April 2023.
- ↑ "10th National Assembly Members - Voter - Validating the Office of the Electorate on Representation". orderpaper.ng. Retrieved 3 September 2024.
- ↑ "Hon. Darlington Nwokocha | Isiala Ngwa North/South Federal Constituency". National Assembly. Retrieved 2 April 2023.
- ↑ Ogundapo, Abdulqudus (4 November 2023). "Appeal Court sacks Senate minority whip". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2 December 2023.
- ↑ Chibuike, Daniel (4 November 2023). "Appeal Court sacks Senate Minority Whip Nwokocha". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2 December 2023.
- ↑ Arogbonlo, Israel (5 November 2023). "Appeal Court sacks Senate Minority Whip, Nwokocha". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2 December 2023.
- ↑ "PDP's Akobundu Sworn In As Abia Senator".