Dauda Kahutu Rarara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Dauda Kahutu Rarara
Dauda Kahutu Rarara.jpg
Haihuwa Dauda
Jihar Katsina, Nigeria
Matakin ilimi Almajiranci
Aiki Mawaƙi
Shekaran tashe 2010 har wayau

Dauda Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara an haife shine a ( jihar Katsina ) shahararren mawaƙin siyasa ne a Nijeriya, mawaƙi kuma marubucin waƙa,[1] wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen rera waƙoƙin siyasa ga ƴan siyasar All Progressive Congress a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2015, musamman ma ga shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari[2] da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari .[3]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifeshi ne a jihar Katsina a wani kauye da ake kira Kahutu, Yayi karatun Alqur'ani a makarantar Almajiranci, wata hanyar gargajiya ce ta Hausawa ta koyon addinin Musulunci .

Siyasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Rarara ya kasance sananne ne yayin babban zaben Najeriya na 2015, lokacin da yake rera wakoki da dama ga Muhammadu Buhari da kuma adawa da shugabancin Goodluck Jonathan a galibin wakokin nasa. A watan satumba na 2020, Rarara ya nemi gudummawa daga masoyan Muhammadu Buhari, don tura masa Naira dubu daya don sakin bidiyon minti biyu na yabon Muhammadu Buhari, cikin kasa da awanni 48 Ya karbi Naira miliyan 57 don sakin wakar wacce Ya yaba Muhammadu Buhari.

Sukar[gyara sashe | Gyara masomin]

Wasu fusatattun matasa sun afkawa Rarara yayin da yake daukar bidiyo a jihar Katsina. Ana zargin sa da wawure Naira Miliyan 100 da jam'iyyar siyasa ta All Progressive Congress ta ba wa duk wadanda ke rera wakoki ga kungiyar siyasa.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]