Dennis Oguerinwa Amadi
11 ga Yuni, 2019 - District: Ezeagu/Udi
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 District: Ezeagu/Udi | |||||
| Rayuwa | |||||
| Haihuwa | 1968 (57/58 shekaru) | ||||
| ƙasa | Najeriya | ||||
| Sana'a | |||||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||||
| Imani | |||||
| Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party | ||||
Dennis Oguerinwa Amadi ɗan siyasan Najeriya ne. Ya kasance memba wanda ke wakiltar mazabar Ezeagu / Udi a Majalisar Wakilai[1][2][3]
Rayuwa ta farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Dennis Oguerinwa Amadi an haife shi a shekarar 1968, kuma ya fito ne daga Jihar Enugu. Ya fara karatun firamare da sakandare a Makarantar Christ High School, Abor, sannan ya kammala karatunsa a shekarar 1986 a Boy's High School, Uzalla. A shekarar 1991, ya kammala karatu a Jami'ar Benin tare da samun digirin farko (Bachelor's Degree) a fannin Kimiyyar Kwamfuta (Computer Science), daga bisani kuma ya samu digirin MBA (Master of Business Administration) daga wannan jami'a.[4][5]
Ayyukan siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A shekara ta 2015, ya gaji Ogbuefi Ora Ozomgbachi don a zabe shi a cikin Majalisar Tarayya a karkashin Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP). An sake zabarsa a shekarar 2019 don wa'adi na biyu.[4] Kafin aikinsa na siyasa, ya yi aiki a bangaren banki sama da shekaru ashirin.[5][6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://citizensciencenigeria.org/public-offices/persons/dennis-oguerinwa-amadi
- ↑ https://citizensciencenigeria.org/public-offices/persons/dennis-oguerinwa-amadi
- ↑ https://citizensciencenigeria.org/public-offices/persons/dennis-oguerinwa-amadi
- 1 2 "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2025-01-03. Cite error: Invalid
<ref>tag; name ":0" defined multiple times with different content. - 1 2 "Hon. Dennis Amadi biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2025-01-03. Cite error: Invalid
<ref>tag; name ":1" defined multiple times with different content. - ↑ Nigeria, Media (2018-06-05). "Biography Of Dennis Amadi". Media Nigeria (in Turanci). Retrieved 2025-01-03.