Digiri
Appearance
Digiri matakin karatu ne da yake gaba da sakandare. A Nijeriya, ana karatun digiri ne a jami'o'i ko kuma kwalejojin ilimi waɗanda suke da haɗin guiwa da wasu Jami’o’i.[1]
Nau'ukan Digiri Da Ake Bayarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ana karatun digiri a fanni daban-daban. Wasu daga cikinsu su ne:
- Digiri a fannin Hausa (B.A. Hausa)
- Digiri a fannin koyarwa da Hausa (B.A. Ed. Hausa)
- Digiri a fannin kimiyya
- Digiri a fannin fasahar gine-gine
- Digiri a fannin ilimin kwamfuta
- Digiri a fannin ilimin harkokin noma
- Digiri a fannin zamantakewa
- Digiri a fannin likitanci
- Digiri a fannin ilimin halitta
- Digiri a fannin kimiyyar harsuna[2]
Matakan Digiri
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai fitattun matakan digiri guda uku. Su ne:
- Digirin farko (bachelor's degree)
- Digiri na biyu (masters
- Digiri na uku (PhD)[3]
Amfanin Karatun Digiri
[gyara sashe | gyara masomin]Amfanin karatun digiri suna da yawa. Daga ciki akwai:
- Samun ilimi da ƙwarewa a wani fanni na musamman.
- Samun ƙwarewar rayuwa da zamantakewa.
- Wayewa
- Buɗewar ido na ganin damarmaki da hanyoyin rayuwa
- Samun ƙwarewar dogaro da kai
- Samun damar neman aiki da takardun karatu[4]
Wasu Jami'o'i a Nijeriya Da Ake Karatun Digiri a Fannin Hausa
[gyara sashe | gyara masomin]Jami'o'i a Nijeriya inda ake karatun digiri na Hausa sun haɗa da:
- Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato (UDUSOK)
- Jami'ar Tarayya ta Gusau (FUGUS)
- Jami'ar Bayero Kano (BUK)
- Jami'ar Ahmadu Bello Zariya (ABU)
- Jami'ar Jahar Kaduna (KASU)[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.britannica.com/topic/degree-education
- ↑ https://www.nuffic.nl/en/education-systems/nigeria/higher-education
- ↑ https://www.snhu.edu/about-us/newsroom/education/college-degree-levels
- ↑ https://www.snhu.edu/about-us/newsroom/education/why-is-college-important
- ↑ https://www.amsoshi.com/2020/11/hausa-gagara-gasa.html