Disamba 2020 Kisan kiyashi na Gijet
| Kisan kiyashi na Gijet | |
|---|---|
| Wani bangare na Yaƙin Tigray | |
Yanayin Gijet a Tigray (Ethiopia)
| |
| Wurin da yake | Gijet (Tigrinya), Yankin Tigray, Habasha |
| Ranar | 30 Disamba 2020 |
| Manufar | Tigrayans |
Irin hari
|
|
| Mutuwa | Fararen hula 21 |
| Masu aikata laifin | Sojojin Tsaro na Habasha |
Kisan mummuke ko kiyashi na Gijet a watan Disamba na shekara ta 2020 wani kisan kiyashi ne wanda ya faru a Gijet (Tigrinya: ጊጀት) a Yaƙin Tigray na Habasha a lokacin Yakin Tigray, a ranar 30 ga Disamba shekara ta 2020. Gijet ita ce tsakiyar garin woreda Saharti, yankin kudu maso gabashin Tigray .
Kisan mummuke/kiyashi
[gyara sashe | gyara masomin]Dakarun Sojojin Tsaro na Habasha (ENDF) sun kashe matasa kimanin 21, ciki har da yaro dan shekara bakwai a Gijet (SE Tigray) a ranar 30 ga Disamba shekara ta 2020.
Kisan kiyashi da dakarun sojojin Habasha da Eritrea suka yi a yakin Tigray shine
(1) fansa lokacin da suka rasa yaƙi;
(2) don tsoratar da kuma fitar da bayanai game da inda shugabannin TPLF suke;
(3) kisan da ake zargi da 'yan bindigar TDF; da kuma
(4) tsoratar al'ummar Tigray gaba ɗaya kamar yadda aka yi kisan kiyashi a cikin majami'u.[1]
Wa'inda suka aikata kisan
[gyara sashe | gyara masomin]Dimtsi Woyane ya ba da rahoton wadanda suka aikata wannan kisan kiyashi sune dakarun sojojin Habasha.
Wadanda aka azabtar
[gyara sashe | gyara masomin]"Tigray: Atlas of the humanitarian situation" ya ambaci mutane guda 21 da aka kashe a wannan kisan mummuken ko na kiyashi.
Yumkurin mataki
[gyara sashe | gyara masomin]"Tigray: Atlas of the humanitarian situation", wanda ya rubuta wannan kisan mummuke ko na kiyashi ya sami kulawar hanyoyin watsa labarai na duniya, musamman game da Annex A, wanda ya lissafa kisan kiyashin a cikin Tigray War.
Bayan watanni na musantawa daga hukumomin kasar Habasha cewa kisan kiyashin ya faru ne a Tigray, an sanar da bincike na hadin gwiwa da OHCHR da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Habasha suka yi a watan Maris na 2021.
Fadad bincike
[gyara sashe | gyara masomin]- Kisan kai da kisan kiyashi a Yakin Tigray
- Jerin lokaci na Yakin Tigray - Disamba 2020
- Fabrairu 2021 Kisan kiyashi na Saharti-Samre, ciki har da wasu mutane kimanin 120 da aka kashe a Gijet
- Maris 2021 Kisan kiyashi na Saharti-Samre, ciki har da wasu mutane guda 123 da aka kashe a Gijet
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ The World radio (2 April 2021): Counting the victims in Tigray[dead link]
Haɗin waje
[gyara sashe | gyara masomin]Samfuri:Tigray conflict13°19′34″N 39°10′26″E / 13.32607°N 39.17393°E