Jump to content

Walter Miller

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Dr Miller)
Walter Miller
Rayuwa
Haihuwa Honiton (en) Fassara, 22 ga Maris, 1872
ƙasa Birtaniya
Mutuwa Jos, 27 ga Augusta, 1952
Makwanci Jos
Sana'a
Sana'a Mishan da mai aikin fassara
Sarkin Zazzau Aliyu ɗan Sidi da Dr Walter Miller

Dr. Walter Richard Samuel Miller Wanda aka fi sani Dr.Miller(an haife shi a 1872 – ya rasu 27 ga Agusta, 1952) ya kasance mishanin Kirista daga Church Missionary Society wanda ya shahara a Najeriya, musamman Arewacin ƙasar. Shi ne wanda ya kafa al’ummar mishan ta Wusasa dake Zaria, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen fassara Littafin Baibûl zuwa harshen Hausa.

[1]

Rayuwa ta farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Dr. Miller a shekara ta 1872 a Burtaniya. Ya karanci ilimin likitanci da na addini kafin ya tafi aikin mishan a Afirka.[2]

Zuwa Najeriya da Aikin Mishan

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekarar 1900, Dr. Miller ya zo Najeriya tare da tawagar Bishop Tugwell domin yada bishara a Arewacin Najeriya. Bayan ƙalubale da suka fuskanta a Kano, a shekarar 1902 sun sami izinin Sarkin Zazzau, Aliyu Kwasau, Miller da abokinsa Bargery su kafa sansani a Zaria. Daga nan ne Dr. Miller ya kafa sansanin Wusasa, wanda ya zama cibiyar mishan da makarantu da asibitoci.[3]

Fassarar littafin Bible

[gyara sashe | gyara masomin]

Dr. Miller ya jagoranci aikin fassarar Littafin Bible zuwa harshen Hausa tare da taimakon J.T. Umar da P.A. Yusuf. Wannan fassarar an kammala ta a shekara ta 1931 kuma aka wallafa ta a shekara ta 1932 wannan fassara ta taimaka wajen yada Addinin Kiristanci a tsakanin Hausawa.

Haduwa da Isawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi hulɗa da ƙungiyar (Isawa) wata ƙungiyar Musulmai inda suka yarda ya koyar da su daga Littafin Bible bayan rasuwar jagoransu Malam Yahaya a 1913.

Dr. Miller ya rasu a shekarar 1952, kuma an binne shi a St. Bartholomew’s Church da ke Wusasa. Har yanzu Wusasa tana daga cikin wuraren da ke nuna haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci a Najeriya.

  1. name = https://www.cambridge.org/core/services/aop-cambridge-core/content/view/266AA9541A9D731EB734538344781556/S0036930600040801a.pdf
  2. name= https://books.google.com.ng/books/about/Walter_Miller_1872_1952.html?id=smcmAQAAIAAJ&redir_esc=y
  3. name=https://dacb.org/stories/nigeria/miller-wr-samuel/