Jump to content

Wata

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Duniyar wata)
Wata 
Observation (en) Fassara
Nisa daga duniya 385,000.5 km, 356,565 km da 406,464 km
Apparent magnitude (en) Fassara −12.74
Parent astronomical body (en) Fassara Duniya
Suna saboda haske
Orbit (en) Fassara
Apoapsis (en) Fassara 405,500 km
Periapsis (en) Fassara 363,300 km
Semi-major axis of an orbit (en) Fassara 384,400 km
Orbital eccentricity (en) Fassara 0.0567
Orbital period (en) Fassara 27.321661 rana
Synodic period (en) Fassara 29.530589 rana
Orbital inclination (en) Fassara 5.145 °
Physics (en) Fassara
Radius (en) Fassara 1,737.1 km
Diameter (en) Fassara 3,476.2 km
Flatness (en) Fassara 0.00125
Yawan fili 37,930,000 km²
Volume (en) Fassara 21,968,000,000 m³
Nauyi 73.4767 Yg
Mass density (en) Fassara 3.344 g/cm³
Effective temperature (en) Fassara 95 K
390 K
Albedo 0.136
Farawa 4,527 million years BCE
sabon wata
Sabon wata da tauraruwa a sararin samaniya
wata a sama mai cikakken girma ba saboba
taswira wata
hasken wata
Moon

Wata: (alama ce:☾) babbar fitilla ce wadda Allah (S W A) maɗaukakin sarki ya halitta daga cikin gungun taurarin da ke a sararin subuhana mai girma, ya sanya ta zama fitilar da ke haskaka sararin duniya yayin da duhu ya baibaye sararin samaniya. Akan ce idan rana ta fito.tafin hannu bai iya kareta. Mallam kimiya sun bayayana cewa wata baya iya samar da haskensa sai dai Rana tahas kashi

moon
Moon
Moon
Moon

Ta ina wata yake samo haskensa

[gyara sashe | gyara masomin]
Cikakken hoton wata
moon
moon

Hakika kamar yadda binciken masana ilimin kimiyya ya tabbatar da cewa wata ya na samun hasken sa ne daga hasken rana wato abin da ake kira reflection a turance.

Ƙaruwar takun-saƙa tsakanin Amurka da tarayyar Soviet, bayan yaƙin duniya na biyu, ya haifar da fargabar cewa sararin samaniya zai koma fagen yakin soji.

Babban muhimmin bangare na yarjejeniyar shi ne hana aika makaman nukiliya zuwa sararin samaniya. Kasashe 100 ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya.

Amma rige-rigen da ake yi na kankane sararin samaniya a halin yanzu ya bambanta da na wancan lokacin.

Babban abin da ya bambanta shi ne ba a taƙaita aika kumbo duniyar wata ga kasashe kadai ba , har da kamfanoni masu zaman kansu.

A watan Janairu, wata tawagar masana ta Amurka mai zaman kanta ta sanar da cewa za ta dauki DNA na mutane , da abubuwan sha zuwa duniyar wata. Sai dai yoyon mai ya hana su kaiwa inda aka nufa.

Sai dai hakan ya haifar da muhawara game da tanade-tanaden yarjejeniyar sararin samaniya, da kuma yadda irin wannan yarjejeniyar za ta yi amfani ga al'umma.

"Mun fara aika wasu abubuwa zuwa duniyar wata don kawai za mu iya yin hakan,ba tare da bin ƙa'ida ko wani tsari ba" in ji Michelle Hanlon, lauya kan sararin samaniya.

Ta ƙara da cewa " watan ya dawo wajenmu shi ya sa muka fara ɓata duniyarsa."

Duk da yadda kamfanoni masu zaman kansu ke kan gaba kan batun duniyar wata, amman har yanzu ƙasasshe na rige-rige kan hakan. Farfesa Saeed Musharr daraktan cibiyar ƙa'idoji da dokokin sararin samaniya ta Birtaniya ya ce dole ne kowace ƙasa ta samu izini kafin ta iya aika wani abu zuwa sararin samaniya.

Duk da cewa duniyar wata a keɓe take, amman tana dauke da ma'adanai da suka hada da kasar da ba kasafai aka fiye samun ta ba, iron, titanium, da helium, wadanda ake amfani da su wajen kera komai tun daga na'urori masu karfin gaske zuwa na'urorin asibiti da likitoci ke amfani da su.

An yi ƙiyasin cewa albarkatun da ke duniyar wata sun zarce malala gashin tunkiya, hakan ya sanya wasu ke kallon wurin a matsayin inda za su samu kudi masu yawa, sai dai wannan wani abu ne da zai dauki lokaci.

A shekarar 1979, wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa ta bayyana cewa babu wata ƙasa ko ƙungiya da ke da haƙƙin mallakar albarkatun duniyar wata. Sai dai yarjejeniyar ba ta samu karbuwa sosai ba, domin kasashe 17 ne suka shiga cikinta, ciki har da kasar Amurka da ta kai ga duniyar wata.

Amurka ta ba da wata doka a 2015 inda ta ba wa 'yan kasarta da kamfanoni damar hakowa, amfani da kuma sayar da albarkatun sararin samaniya.

A cikin duniyar wata akwai ruwa daskararre a cikin ramuka.

Mutane za su iya shan ruwa, za kuma a iya samar da iskar oxygen, haka kuma ƴan sama jannati na iya amfani da ruwan wajen yin mai na jirginsu wanda zai ba su damar zuwa duniyar Mars da gaba da can.

Amurka na ƙoƙarin ganin ta samar da ƙa'idoji na bincike da gano albarkatun da ke duniyar wata.

Sama da ƙasashe arba'in ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar. Sai dai ƙasar China ba ta cikin ƙasashen da suka amince da yarjejeniyar, saboda ƙasashe da dama na ganin bai kamata wata ƙasa ce za ta sanya dokar da ta shafi duniyar wata ba.