Durbar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Mahayin doki a bikin Durbar a birnin Kano shekarar 2006
Bikin Dutbar a Birnin Bidda na jahar Neja a Arewacin Najeriya

Hawan Durbar ko Bikin Durbar wani tsohon bikin al'adane wanda yake gudana shekara-shekara a wasu daga cikin jahohin Najeriya. Wannan bikin yana nuna kawo karshrn watan Ramadana ne da kuma gabatar da bikin karamar Sallah da babbar Sallah, ranakun hutun musulmai. Ana fara Dutbar ne da gabatar da Sallar Idi sannan kuma sai mahaya su fara sukuwa da dokuna, da yan rakiyar makada tare da kawo karshen sa a Fadar sarki. Bikib Durbar anfi sanin sa ne a biranen Kano, Sakkwato, Zariya, Katsina da Bida kuma yana jawo hankulan yan yawon bude ido.

Tarihin Durbar[gyara sashe | Gyara masomin]

Durbar a Bauchi
Durbar a Zaria
Durbar a Kano


Turawan mulkin mallaka ne suka kawo bikin Durbar a Najeriya. Amma asalin kalmar Durbar tazo ne dagaharshen Farisa daga bukuwan nuna goyon baya ga saraunia Biktoriya amatsayin Sarauniyar Indiya bayan shigar turawan mulkin mallaka na Birtanya kasar ta Indiya a 1877. An fara bikin durbar na farko ne a Najeriya cikin shekarar 1911, daga baya bikin yaci gaba ashekarun 1924, 1925, 1948, 1960 da 1972. Bikin yaci gaba a kasar har ya zuwa yanzu kuma yana daga cikin muhimman bukukuwa a Arewacin Najeriya.

Bukukuwan[gyara sashe | Gyara masomin]

An gabatar da bikin Durbar a bankin 2nd World Bank da kuma African Festival of Arts an Culture anfi sanin bikin da FESTAC 77. A hankali turawa suka cusa son bikin na durbar domin su karama sojoji kaimi wajen hawan dokuna tare da kara kawata Bikin Sallah.