E.K. Nyame

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
E.K. Nyame
Rayuwa
Haihuwa Kwahu South District, 24 Disamba 1927
ƙasa Ghana
Mutuwa ga Augusta, 1977
Karatu
Harsuna Yaren Akan
Sana'a
Sana'a guitarist (en) Fassara da mai rubuta kiɗa
Imani
Addini Katolika

Emmanuel Kofi Nyame, wanda aka fi sani da EK Nyame (An haife shi 24 ga watan Disamba, shekarar 1927 - ya mutu a watan Agusta shekarar 1977), an ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin “ubanni” na mawakan zamani na Ghana.[1][2] Marubuci ne ɗan ƙasar Ghana, mawaƙa, wanda ya kafa E.K. banda Akan Trio.[3] An sanshi a matsayin jagaba na Manyan waƙoƙi a yaren akan matakan kide -kide.[4]

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi E.K. Nyame a Kwahu Dukomang. Ya zama babban madugu, jagoran ƙungiyar rayuwar makarantan a Adabraka Roman katolika a Accra. Ya kasance memba na mawaƙan cocin da aka zaɓa a Cocin Katolika na farko a Accra. Ya gaji jita na wani dan uwansa wanda aka sanya shi cikin yakin duniya na biyu da tilas.[3]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya koyi salon wasan jita na Appiah Agyekum a rediyo kuma daga baya a shekarar 1947, ya shiga ƙungiyar Appiah Agyekum. Daga baya ya bar ƙungiyar don ƙirƙirar ƙungiyar E.K. shekaru biyu bayan ya shiga ƙungiyar Appiah Agyekum.[5]

An zabi kungiyar E.K. don rakiyar Firayim Ministan Ghana, Dakta Kwame Nkrumah, zuwa Laberiya a shekara ta alif 1952. A wannan shekarar E.K. ya kafa ƙungiya na kide kide guda uku, tare da haɗe shi da ƙungiyar makaɗansa da E.K. Band, mai suna kungiyar Akan Trio. Ƙungiyoyin kide-kide na farko da aka kafa suke waƙoƙin turancin Ingilishi da aka shigo da su daga Amurka da Ingila, kuma mazauna Turai suka buga su. Waƙar ita ce kiɗan gidan rawa na yamma, saurin, foxtrots da ragtimes waɗanda aka koya daga Sojojin Burtaniya masu yawo.[6]

Akan Trio ya rera wakokin 'highlife' a Akan shirye -shiryen biki wanda Nyame da kansa ya shirya; ba a taba yin haka ba. Wakokinsa da wasanninsa sun goyi bayan yunkurin Nkrumah na samun 'yancin kai a shekarun ƙarshe na mulkin mallaka na Biritaniya.[6]

A shekarar 1975, Nyame ya yi rikodin din diski 400 78 rpm na kamfanoni kamar Westca Decca, 'Queenophone' da Muryar Jagorarsa (HMV) suna gine gine a Yammacin Afirka.[6] Nyame ya mutu a watan Agustan 1977. An yi masa jana'izar jiha tare da shimfida gawar a kan gadon zinari. An kiyasta cewa mutane 10,000 ne suka halarci jana'izarsa.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "E.K. Nyame". Oxford Reference (in Turanci). Retrieved 2020-08-06.
  2. Congress, The Library of. "LC Linked Data Service: Authorities and Vocabularies (Library of Congress)". id.loc.gov. Retrieved 2020-08-06.
  3. 3.0 3.1 "Ghana's Highlife Music Collection: E.K. Nyame". www.fondation-langlois.org. Retrieved 2020-08-06.
  4. Collins, Edmund John (1987). "Jazz Feedback to Africa". American Music. 5 (2): 176–193. doi:10.2307/3052161. ISSN 0734-4392. JSTOR 3052161.
  5. Collins, John (1985). Musicmakers of West Africa (in Turanci). Lynne Rienner Publishers. ISBN 978-0-89410-075-8.
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 "E.K. Nyame | Biography & History". AllMusic (in Turanci). Retrieved 2020-08-06.

Kara karantawa[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin waje[gyara sashe | gyara masomin]

  • Cool time with E.K. Nyame and his blues