Jump to content

Ebenezer Adam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ebenezer Adam
Member of the 2nd Parliament of the 1st Republic of Ghana (en) Fassara

9 ga Yuni, 1965 - 24 ga Faburairu, 1966
Election: 1965 Ghanaian parliamentary election (en) Fassara
Member of the 1st Parliament of the 1st Republic of Ghana (en) Fassara

1960 - 1965
Election: 1956 Gold Coast legislative election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Tamale, 1919
Mutuwa 29 ga Augusta, 2011
Karatu
Makaranta Achimota School Teachers' Training Certificate (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Malami
Imani
Addini Kiristanci
Musulmi
Jam'iyar siyasa Convention People's Party (en) Fassara

Ebenezer Adam (1919–2011) malami ne kuma ɗan siyasa ɗan ƙasar Ghana. Ya kasance ɗan majalisa mai wakiltar Gulkpegu Nanton daga shekarun 1960 zuwa 1965 da kuma ɗan majalisa mai wakiltar Tamale daga shekarun 1965 zuwa 1966. Ya kuma riƙe muƙamin kwamishinan yanki (Ministan yankin) na yankin Arewa daga shekarun 1964 zuwa 1966.[1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Adam a shekara ta 1919 a Tamale a Arewacin Ghana (sai Gold Coast). Ya yi karatun sa na farko a Makarantar kwana ta Gwamnati da ke garin Tamale daga shekarun 1927 zuwa 1934.[2] Ya wuce Kwalejin Achimota kuma ya yi karatu a can daga shekarun 1936 zuwa 1939. [3]

Aiki da siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Adam yayi aiki a matsayin malami a makarantun mission Methodist dake Asokore, Bekwai, Kumasi da kuma Tamale daga shekarun 1940 zuwa 1949. Ya bar aikin koyarwa ya shiga siyasa ya shiga jam’iyyar Convention People’s Party.[4] A shekarar 1950 aka naɗa shi sakataren yaɗa farfaganda na jam’iyyar na yankin Arewa da na sama. [3] Ya yi aiki a wannan matsayi daga shekarun 1950 zuwa 1957.[5][3] A shekarar 1957 ya kasance memba na tawagar Ghana ta farko zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya. [3] Ya kuma kasance cikin tawagar Ghana a shekarar 1959 da 1960 zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya. [5] Ya zama alkalin kotun ƙaramar hukuma a shekarar 1960 kuma a wannan shekarar ne aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisa don wakiltar mazaɓar Gulkpegu Nanton. [5] Ya wakilci mazaɓar a majalisa daga shekarun 1960 zuwa 1965. A shekarar 1965 ya zama ɗan majalisar wakilai ta Tamale. A shekarar 1964 aka naɗa shi Kwamishinan Yanki (Ministan yanki) na yankin Arewa. Ya yi wannan aiki har zuwa shekara ta 1966 lokacin da aka hambarar da gwamnatin Nkrumah. [3]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Adamu ya yi aure yana da ‘ya’ya 12. [3] Abin sha'awar sa su ne karatu da tafiya.

Ya rasu ne a ranar 29 ga watan Agustan 2011 a asibitin koyarwa na Tamale bayan gajeruwar rashin lafiya. [3]

  • Jerin sunayen 'yan majalisar da aka zaba a zaben 'yan majalisar dokokin Ghana na 1965
  1. Ghana Year Book. Graphic Corporation. 1961. p. 12.
  2. "Ghana Year Book". Daily Graphic. 1956. p. 155.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 3.5 3.6 "Co-founder of CPP, Ebenezer Adam to be buried in Tamale". Ghana Business News. 11 October 2011. Retrieved 6 November 2019. Cite error: Invalid <ref> tag; name "EBENEZER ADAM" defined multiple times with different content
  4. Ghana Year Book. Graphic Corporation. 1962. p. 12.
  5. 5.0 5.1 5.2 Ghana Year Book. Graphic Corporation. 1977. p. 179.