Jump to content

Ebun Clark

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ebun Clark
Rayuwa
Cikakken suna Ebun Odutola
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a Farfesa

Ebun Clark ( née Odutola ) malami ne kuma farfesa na farko a Najeriya a fannin fasahar wasan kwaikwayo. [1]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Clark a cikin dangin Odutola na Ijebuland. [2] Mahaifinta shine Jimoh Odutola, dan kasuwa kuma kanin Adeola Odutola . [1]

Ta karanta magana da murya a Rose Bruford College of Theater and Performance, Sidcup, London.

Ta kasance daya daga cikin malaman farko na makarantar wasan kwaikwayo a jami'ar Ibadan a shekarar 1963. [2] [3] A 1965 ta koma sashen turanci a jami'ar Lagos aka nada ta shugabar cibiyar nazarin al'adu a shekarar 1983. Ta yi ritaya daga jami'a a 1991. [2]

Ta hadu da John Pepper Clark, wani mawaki dan Najeriya wanda a lokacin ya kasance jami'in bincike a Cibiyar Nazarin Afirka ta Jami'ar Ibadan a lokacin da take ba da lacca a makarantar wasan kwaikwayo. Sun yi aure a ranar 4 ga Afrilu 1964 a wani ƙaramin biki a Cotonu, Jamhuriyar Benin . Iyalinta sun yi adawa da aurenta da JP Clark saboda bambancin kabilanci kasancewar ita Ijebu daga kudu maso yammacin Najeriya yayin da yake Ijaw daga Neja-Delta . A dalilin haka ne suka yi ta kai ruwa rana a Cotonu. [2]

Jami'ar Leeds ce ta dauki nauyin bincikenta game da Hubert Ogunde da aikinsa.

Ta hada PEC Reparatory Theater a 1982 a Legas tare da JP Clark. [4]

Bibiyar Tarihi

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Hubert Ogunde: The Making of Nigerian Theatre (1979) [5]
  1. 1 2 "Jimoh Odutola, akọni oníṣòwò tí kò kàwé, àmọ́ táwọn Ààrẹ orílẹ̀-èdè ń ké sí láti wá dá iléesẹ́". BBC News Yorùbá (in Yarbanci). 2021-03-19. Retrieved 2021-08-12. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. 1 2 3 4 Osofisan, Femi (2020-07-09). "J. P. and Ebun Clark: A Love Story -". The NEWS. Archived from the original on 2020-07-12. Retrieved 2021-08-12. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  3. Osofisan, Femi (2018-11-11). "Ebun Clark: The matriarch and her two Idols". The Guardian Nigeria News – Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2021-08-12. Retrieved 2021-08-12.
  4. "Clark, Ebun". Archived from the original on 2021-08-13.
  5. Klíma, Vladimír (1982). "Ebun Clark, Hubert Ogunde: The Making of Nigerian Theatre (Book Review)". Archiv Orientální. Praha. 50: 377–378. ProQuest 1304096486.