Jump to content

Edith Balas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Edith Balas
Rayuwa
Haihuwa Cluj-Napoca (en) Fassara, 1929 (94/95 shekaru)
Karatu
Makaranta University of Pittsburgh (en) Fassara
Sana'a
Sana'a art historian (en) Fassara
Employers Carnegie Mellon University (en) Fassara

Edith Balas farfesa ne na Tarihi na Art Art, College of Humanities & Social Sciences a Jami'ar Carnegie Mellon a Pittsburgh, Pennsylvania. An haife ta a ranar 20 ga watan Yuni, shekara ta 1929 a Cluj, Romania, wadda ta tsira daga Holocaust, farfesa na fasaha kuma masaniyar tarihi

Tarihin Rayuwarta[gyara sashe | gyara masomin]

Ita ce gwauruwar marigayi masanin lissafi Egon Balas, wanda farfesa ne a Carnegie Mellon.

Babban wuraren da Balas tafi sha'awa shine fasahar zamani ashekara ta (1890-1960), zane-zane da sassaka, da fasahar Renaissance na Italiya. [1] [2] [3] Acikin shekara ta 2003, ta shirya wani nuni agidan kayan gargajiya na Frick, da yawa a Pittsburgh, Paris, New York da Budapest. Ta kasance tana koyarwa a Jami'ar Carnegie Mellon tun shekara ta 1977, kuma itace Adjunct Professor of History of Art and Architecture a Jami'ar Pittsburgh .

Balas kuma wanda ta tsira daga Holocaust, an tura ta sansanin mutuwar Nazi Auschwitz . Acikin Tsuntsaye a cikin Jirgin: Memoir na Mai tsira da Masanin Ilimi, Balas tabada labarinta na fuskantar yanayi mara kyau da kuma zama abin da ta bayyana a matsayin "masaniyar tsira." Balas ta sanya wa tarihinta suna "Tsuntsu a cikin Jirgin sama" bayan sanannen sassaka na Constantin Brâncuși mai suna iri ɗaya. "Ina ganin hakan alamar rayuwata ce," injita.

Bayan yaƙin, hukumomin gurguzu sun ɗaure mijinta har na tsawon shekaru uku, a lokacin Balas ya rene ’ya’yansu mata biyu. Ta sami MA a Falsafa daga Jami'ar Bucharest a shekara ta 1952. Daga nan tayi hijira zuwa Amurka tare da mijinta, kuma ta sami digiri na biyu acikin Tarihin Arts daga Jami'ar Pittsburgh a shekara ta 1970 da Ph.D. a shekarar 1973.

Ayyukanta[gyara sashe | gyara masomin]

  • Edith Balas, "Michelangelo's Medici Chapel: A New Interpretation", Philadelphia, 1995

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Empty citation (help)
  2. Empty citation (help)
  3. Empty citation (help)