Eleanor Nwadinobi
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Jihar Abiya, |
| ƙasa |
Najeriya Jamaika |
| Karatu | |
| Makaranta |
St Louis Grammar School Mokola (en) Jami'ar Najeriya, Nsukka Jami'ar Ibadan Cibiyar Harkokin Jama'a ta Turai don 'Yancin Dan Adam da Dimokuradiyya |
| Harsuna | Turanci |
| Sana'a | |
| Sana'a |
likita da Women's Health Activist (en) |
| Employers |
South East Kent Health Authority (en) |
| Eleanor Nwadinobi | |
|---|---|
| Matakin ilimi |
Queen's school, Enugu Saint Louis grammar school, Ibadan The international school, university of Ibadan University of Nigeria, Nsukka European inter-university center, Venice |
| Aiki |
Medical doctor Women health activist |
Eleanor Nwadinobi likita ce ta Najeriya kuma mai fafutukar kula da lafiyar mata. [1] [2] Ita ce 'yar Najeriya ta farko da aka fara zaɓa a matsayin shugabar kungiyar mata ta likitoci ta duniya.[3] [4]
Asali
[gyara sashe | gyara masomin]Mahaifin Eleanor ɗan Jihar Abia ne, a Najeriya, kuma mahaifiyarta 'yar kasar Jamaica ce. Dukkansu sun hadu ne a London lokacin mahaifinta yana karatun likitan dabbobi a Jami'ar London ita kuma mahaifiyarta a lokacin tana koyon horan zama ma'aikaciyar jinya.
Ta halarci makarantu da yawa saboda aikin mahaifinta da katsewar Yaƙin basasar Najeriya. Ta halarci Makarantar Queen, a Enugu; Makarantar Saint Louis Grammar, a Ibadan; da International School , a Jami'ar Ibadan. Ta sami digirin ta na farko a fannin kiwon lafiya a Jami'ar Najeriya, Nsukka. Ta sami digiri na biyu a fannin 'yancin dan adam a Cibiyar Jami'o'in Turai ( European Inter-University Centre) da ke Venice, Italiya.[5]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi aiki a matsayin magatakarda a Burtaniya(UK). Ta yi aiki tare da asibitoci a ƙarƙashin Hukumar Lafiya ta Kudu maso Gabas Kent, ciki har da Dover, Folkestone da Ashford. [5] Tayi aiki tare da kungiyoyin kare hakkin dan adam don bayar da shawarwari game da fyade, FGM da sauran ayyukan cin zarafin mata. [6] Ita ce shugabar Windows Development Organization. [7] [8] Ta kasance memba a kwamitin gudanarwa na Yarjejeniya ta kowace mace wadda ta ba da shawarar dokar hana cin zarafi da cin zarafin mutane da aka zartar da ta hada da hukunci kan al'adun gargajiya masu cutarwa ga mata. [9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Eleanor Nwadinobi, fighting for Nigerian women's rights to health and protection". www.who.int (in Turanci). Retrieved 2020-03-11.
- ↑ Adegun, Aanu (2020-03-10). "Buhari receives president of international women organisation". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2020-03-11.
- ↑ "Doctors protest stripping of colleague naked in Abuja". Punch Newspapers (in Turanci). 16 January 2020. Retrieved 2020-03-11.
- ↑ Omotayo, Joseph (2020-03-09). "Nigerian Nwadinobi is head of 100-yr-old int'l group fighting for women's rights". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2020-03-11.
- 1 2 "I was charmed by my husband's focus, humility–Nwadinobi, Medical Women's International Association President-elect". Punch Newspapers (in Turanci). 24 August 2019. Retrieved 2020-03-11.
- ↑ "Foundation adopts entertainment to tackle FGM". Vanguard News (in Turanci). 2018-02-07. Retrieved 2020-03-11.
- ↑ "Violence is a public health emergency — Dr Nwadinobi". Vanguard News (in Turanci). 2019-06-20. Retrieved 2020-03-11.
- ↑ "Not Yet Uhuru with Widows' Rights - Eleanor Nwadinobi". Vanguard News (in Turanci). 2012-07-26. Retrieved 2020-03-11.
- ↑ "Activists Campaign for Treaty to End Violence Against Women". Voice of America (in Turanci). Archived from the original on December 9, 2019. Retrieved 2020-03-11.