Ellen Gwaradzimba
2019 - 15 ga Janairu, 2021
| |||||
| Rayuwa | |||||
| Cikakken suna | Ellen Munyoro | ||||
| Haihuwa |
Gutu (en) | ||||
| ƙasa | Zimbabwe | ||||
| Mutuwa | Harare, 15 ga Janairu, 2021 | ||||
| Makwanci |
National Heroes Acre (en) | ||||
| Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Koronavirus 2019) | ||||
| Karatu | |||||
| Makaranta |
University of Zimbabwe (en) Jami'ar Fort Hare | ||||
| Sana'a | |||||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||||
| Imani | |||||
| Jam'iyar siyasa | ZANU-PF | ||||
Ellen Gwaradzimba (née Munyoro; 25 Disamba 1960-15 Janairu 2021) 'yar siyasar Zimbabwe ce.[1]
Ta yi aiki a matsayin memba na Majalisar Dattawan Zimbabwe kuma a matsayin ministar harkokin larduna ta lardin Manicaland daga shekarun 2018 har zuwa rasuwarta a shekarar 2021.[2]
Gwaradzimba ta mutu ne a ranar 15 ga watan Janairu, 2021, wacce ta kamu da cutar ta COVID-19 yayin ɓarkewar cutar COVID-19 a Zimbabwe, a wani asibiti mai zaman kansa a Harare. [2] Shugaba Emmerson Mnangagwa ne ya ayyana Gwaradzimba a matsayin Jaruma ta Ƙasa. [2]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ellen a gundumar Gutu a shekarar 1960, ta yi makarantar firamare da sakandare a Masvingo. [3] Ta shiga gwagwarmayar neman 'yanci tana da shekaru 16 sannan ta shiga makarantar soja ta Nachigwea da ke Tanzaniya inda ta yi karatun boko.
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ta mutu a ranar 15 ga watan Janairu, 2021 a sakamakon Covid. [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.newzimbabwe.com/manicaland-provincial-minister-gwaradzimba-dies-from-covid-19/
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "Malianga, Gwaradzimba declared national heroes". The Sunday Mail. 2021-01-17. Archived from the original on 2021-10-21. Retrieved 2022-01-03.
- ↑ "Meet Gwaradzimba: The people's person". The Herald (in Turanci). Retrieved 2023-10-28.
- ↑ "Malianga Gwaradzimba declared national heroes". The Sunday Mail. 17 January 2021. Retrieved 28 October 2023.[permanent dead link]