Emmanuel Chukwuma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Emmanuel Chukwuma
Rayuwa
Haihuwa 1954 (69/70 shekaru)
Sana'a

Emmanuel Chukwuma babban bishop (ko archbishop) ne na Cocin Najeriya (Anglican) dake Najeriya.[1] Shi ne Bishop na Diocese na Enugu a halin yanzu kuma babban Bishop na lardin Anglican na Enugu.[2][3] Ya kasance Archbishop tun cikin shekarar 2014.[4][5]

An haifi Chukwuma a Asaba a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta alif 1954. Bayan kammala karatun sakandare ya horar da zama malami. Sannan ya kammala karatun tauhidi a Kwalejin Immanuel ta Ibadan. An naɗa shi a shekarar 1981 kuma ya yi hidima a cocin Christ Church, Ibadan. Ya kuma yi aiki a matsayin Malami ga Archbishop na Najeriya Alherinsa, Most Rev'd Timothy Olufosoye, Primate na Cocin Najeriya na farko; Vicar na St. Paul, Ibadan; kuma a matsayin bishop na Bauchi.[6]

An zaɓe shi a matsayin archbishop na Enugu a babban taron Cocin Najeriya karo na 11, wanda aka gudanar a Cocin Cathedral of the Good Shepherd, Enugu, a cikin watan Satumban 2014.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.anglicancommunion.org/structures/member-churches/member-church/diocese/position.aspx?church=nigeria&dio=enugu&pos=archbishop-of-enugu-province-and-bishop-of-enugu&posID=425
  2. https://www.vanguardngr.com/2020/04/igbo-leadership-in-shambles-archbishop-chukwuma/
  3. https://anglican-nig.org/our-provinces/ecclesiastical-province-of-enugu/
  4. https://guardian.ng/tag/emmanuel-chukwuma/
  5. https://web.archive.org/web/20170221105531/https://anglican-nig.org/60th-birthday-thanksgiving-service-and-25th-year-of-episcopacy-of-the-most-rev-emmanuel-chukwuma-archbishop-elect-of-enugu-province/
  6. https://www.worldanglican.com/nigeria/enugu/the-church-of-nigeria-anglican-communion/the-rt-revd-emmanuel-chukwuma
  7. "Kwafin ajiya" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2022-06-26. Retrieved 2023-03-28.