Jump to content

Emmanuel Ukpong-Udo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Emmanuel Ukpong-Udo
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
Iboro Ekanem
District: Ikono/Ini
Rayuwa
Haihuwa 2 Disamba 1975 (50 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Emmanuel Ukpong-Udo (an haife shi a ranar 2 ga watan Disamba, 1975) [1] ɗan siyasa ne a Najeriya, mai taimakon jama'a kuma wakili na gaskiya a Majalisar Wakilai ta Tarayya a Najeriya. [2] Ya wakilci mazaɓar tarayya ta Ikono / Ini a Majalisar Dokokin Najeriya.[2] Ya kasance Babban tsohon Mataimaki na Musamman (SSA) ga Ministan harkokin kasa, Gidaje da Ci gaban Birane a Najeriya (2014-Mayu 2015), [1] kuma shine jagoran Siyasa na yanzu a ƙaramar hukumar Ikono dake Jihar Akwa Ibom, Najeriya.[1]

Emmanuel Ukpong-Udo yana da farin jini a wajen mutanen mazaɓarsa saboda shirye-shiryen ci gaba da tallafi da yake yi.[3] Ayyukansa na kyautatawa sanannu ne a tsakanin mutanen mazaɓar tarayya ta Ikono / Ini, abokan siyasa [3] da kungiyoyi a Najeriya. A bikin bayar da lambar yabo karo na shida na Leadership Excellence (LEEX), wanda Igbere TV ta shirya, an ba shi kyauta ta Mafi Kyawun Ɗan Majalisar wakilai a fannin Karfafa jama'a.[4]

Bayan siyasa da taimakon jama'a, Emmanuel Ukpong-Udo kwararre ne a fannin tsaro da lafiyar ma'aikata.

  1. 1.0 1.1 1.2 "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2024-11-05.
  2. 2.0 2.1 Utip, Udeme (2023-05-06). "Akwa Ibom: INEC declares YPP candidate winner of Reps seat". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2024-11-05.
  3. 3.0 3.1 Ukpong, Cletus (July 10, 2019). "Nigerian lawmaker appoints 50 aides". premiumtimesng.com. Retrieved 2024-11-06.
  4. Kalu, Nicholas (November 2, 2024). "A'Ibom lawmaker gets award for leadership, humanity ". The Nation.