Engrácia Cabenha
Engrácia Francisco Cabenha (an haife ta a shekara ta alif 1949) jami'iyyar sojan kasar Angola ce sannan kuma ita din mai fafutukar yaki da mulkin mallaka ce. Ita ce mace ɗaya tilo da ta kasance cikin rukunin 'yan kishin kaysa waɗanda, a ranar 4 ga watan Fabrairun 1961, suka mamaye gidajen yarin 'yan mulkin mallaka a Luanda, wanda ya haifar da yakin 'yancin kai na Angola.
Engrácia Francisco Cabenha, wacce kuma aka fi sani da "Sarauniyar (Queen) 4 ga watan Fabrairu" da "Sarauniyar 'Yanci", tana da shekaru 12 kacal a lokacin da ta shiga cikin ayyukan 4 ga watan Fabrairu a 1961, wanda ya haifar da mamaye mulkin mallaka na Luanda gidajen yari.[1]
Don yin haka, sai da ta ci jarrabawar likitanci da ke tabbatar da cewa ita budurwa ce, sannan aka kulle ta a cikin gida har tsawon kwanaki 90, ana yin azumi da shiri na ruhaniya.[1][2]
A ranar 4 ga watan Fabrairun 1961, ita ce mace tilo a cikin mayaka 3,123 da suka mamaye gidajen yarin Luanda, da Emissora Radio Nacional de Angola da hedkwatar Correios de Angola, wacce ta fara gwagwarmayar ‘yantar da Angola.[3][4][5]
Daga baya Engrácia ta shiga kungiyar mata ta dakarun 'yantar da ƙasar Angola (FAPLA), wacce ta taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar yaki da mulkin mallaka na Angola.[3]
Cabenha tana cikin ajiyar kuma tana rike da muƙamin babban janar na rundunar sojojin Angola.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Antigos guerrillas want special treatment". NovaGazeta (in Turanci). Retrieved 2022-04-11.
- ↑ Agualusa, José Eduardo (2007). Estação das Chuvas (in Turanci). Leya. p. 105. ISBN 9789722033794.
- ↑ 3.0 3.1 ""Rainha do 4 e Fevereiro" example for youth". Official Page of the Vice-President of the Republic of Angola (in Turanci). 2018-06-13. Retrieved 2022-04-11.[permanent dead link]
- ↑ "Much blood was shed" (in Turanci). Angola Formativa. Retrieved 2022-04-11.
- ↑ 5.0 5.1 "As Muataas - Por Isilda Alves Coelho by O Toke É Esse". issuu.com (in Turanci). Archived from the original on 2022-04-11. Retrieved 2022-04-11.