Esha Deol
|
|
|
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Mumbai, 2 Nuwamba, 1981 (44 shekaru) |
| ƙasa | Indiya |
| Ƴan uwa | |
| Mahaifi | Dharmendra |
| Mahaifiya | Hema Malini |
| Abokiyar zama | Bharat Takhtani (en) |
| Ahali | Ahana Deol (en) |
| Karatu | |
| Makaranta | Mithibai College (en) Jamnabai Narsee School (en) Kodaikanal International School (en) |
| Harsuna | Harshen Hindu |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo |
| Tsayi | 1.58 m |
| Kyaututtuka | |
| IMDb | nm0219968 |
Esha Deol (an haife ta ranar 2 ga watan Nuwamba, 1981) ƴar wasan kwaikwayo ce ta ƙasar Indiya, wacce ta fi bayyana a fina-finan Hindi. Iyayenta Dharmendra da Hema Malini, ƴan fim ne. Deol ta fara wasan kwaikwayo a wani shirin wasan kwaikwayo mai ban sha'awa Koi Mere Dil Se Poochhe (2002), wanda fim ɗin ya yi silar da ta lashe kyautar lambar yabo ta Filmfare a matsayin rukunin sabuwar shiga-(sabuwar jarumar) da tayi fice a shirin.[1]
Bayan jerin fitowa a wasu fina-finai da ba su yi wani tasiri ba, Deol ta sami nasara a fina-finan; Aayutha Ezhuthu (2004), wasan kwaikwayo na Dhoom (2004) da Dus (2005), fim mai ban tsoro Kaal (2005), da kuma wasan kwaikwayon No Entry (2005). Deol ta koma yin wasan kwaikwayo biyo bayan ja-baya da tayi, tare da fitowa a cikin jerin shirye-shiryen Rudra: The Edge of Darkness (2022) da Hunter Tootega Nahi Todega (2023).
Farkon rayuwa da iyali
[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Esha Deol a Bombay (yanzu Mumbai) a ranar 2 ga Nuwamban 1981. [2][3] Ita ce 'yar' ɗan wasan masana'antar fim ta Bollywood Dharmendra da Hema Malini. Tana da 'yar'uwa mai suna Ahana. Ita ce 'yar'uwar' yan wasan kwaikwayo Sunny Deol da Bobby Deol kuma dan uwan dan wasan kwaikwayo Abhay Deol. [4] Mahaifinta ɗan Punjabi Jat ne, kuma mahaifiyarta 'yar ƙabilar Hindu ce ta Tamil Iyengar Brahmin.[5][6] Tana magana da yaren Tamil tare da mahaifiyarta da 'yar'uwarta.[7][8]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Farkon fim dinta da wadanda suka biyo baya (2002-2003)
[gyara sashe | gyara masomin]
Ta fara fitowa a fim a matsayin wacce ta jagoranci shirin-(lead role) tare da Vinay Shukla's Koi Mere Dil Se Poochhe (2002) a gaban Aftab Shivdasani, tare da Sanjay Kapoor, Jaya Bachchan da Anupam Kher suna taka rawa. Fim ɗin bai yi tasiri ba. Deol ta sami ra'ayoyi mabanbanta daga masu suka ko bitar fim game da rawar da ta taka a shirin. Savera R Someshwar na Rediff.com ya rubuta game da shirin "Esha, na nuna iyawa, wanda hakan kamar girman kai. " [9] Rakesh Budhu na Planet Bollywood ya rubuta "Ba ta da tsoro"[10]
Fim biyu na farko na Deol na 2003: Kucch To Hai da Chura Liyaa Hai Tumne ba suyi tasiri ba. [11] [12]
Deol na ɗaya daga cikin jarumai na JP Dutta mai yawan yaƙi mai suna LOC: Kargil kuma an haɗa ta da jarumi Abhishek Bachchan. Kodayake Deol da duk sauran jarumai ba su iya samun iko sosai ba, ta sami yabo mai mahimmanci dalilin rawar da ta taka a shirin.[13][14] Fim din ya zama na shida cikin fina-finai mafiya samun riba a wannan shekara.[15]
Ci gaba (2004-2008)
[gyara sashe | gyara masomin]
A shekara ta 2004, Deol ta fara fitowa a fina-finai na Tamil, daga cikin ta taka rawa a matsayin malamar Faransanci a fim ɗin siyasa na Mani Ratnam Aayutha Ezhuthu tare da Suriya . Ta sami yabo mai mahimmanci dalilin rawar da ta taka. Sify.com ta bayyana ta a matsayin "mai ban mamaki".[16] Domin cigaba da fitowa a fina-finai na Tamil, Deol ta koyi wasu nau'o'in yaren tare da taimakon Mani Ratnam R. Kannan. Wannan shi ne ɗaya tilo fim ɗin Tamil da ta taɓa fitowa a ciki. Bayan kammala Aaytha Ezhuthu, Deol ta fara yin fim ɗin Hindi mai taken Yuva. [17] A Yuva, Deol ta sake maimaita wannan rawar kuma an haɗa ta da jarumi Ajay Devgn. An saki fina-finai biyu a rana guda, amma fina-finan ba su yi tasiri ba..[18]
Deol a ƙarshe ta sami ci gaba tare da Fim din kamfanin Yash Raj Films 'Dhoom tare da jaruman shirin; Abhishek Bachchan, John Abraham, Uday Chopra da Rimi Sen. Wannan shine aikinta na farko anan, a shirin akwai jaruma Chopra. Fim ɗin ya samu karɓuwa, ya zama fim na huɗu cikin fina-finai mafiya samun riba a wannan shekara.[18] Duk da ƙarancin samun iko a cikin fim ɗin, amma irin rawar da ta taka ya yi silar da aka zaɓe ta cikin jerin masu takarar don lashe kyautar lambar yabo ta IIFA a karo na 6, ta rukunin masu taimakawa jagororin shirin fim a fim ɗin-(Supporting actress).[19]
Sauran ayyukanta
[gyara sashe | gyara masomin]| Personal information | |||
|---|---|---|---|
| Position(s) | Midfielder | ||
| Senior career* | |||
| Years | Team | Apps | (Gls) |
| ?–2001 | Maharashtra | ||
| * Senior club appearances and goals counted for the domestic league only | |||
A lokacin da take makaranta a Makarantar Jamnabai Narsee, tana da sha'awar kwallon kafa kuma tana taka leda a matsayin ƴar wasan tsakiya. Ta kasance kyaftin ɗin tawagar kwallon ƙafa ta makaranta, ta wakilci kwalejin ta a wasan kwallon hannu a matakin jiha. Ta taka leda a matsayin ƴar wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasa kuma an zaɓe ta don buga wa Maharashtra wasa a Babbar Gasar Cin Kofin Kasa a Punjab a shekara ta 2001.[20][21]
Kamar mahaifiyarsu, Esha da 'yar'uwarta suna horar da su a cikin salon rawa na gargajiya..[22] Esha ƙwararriyar ƴar rawa ce ta Odissi kuma ta samu horon ne a Bharatanatyam.[23]
A watan Fabrairun 2020, Deol ta kaddamar da littafinta na farko; Amma Mia! a kan dandamalin Instagram.[24] Littafin na bayanin jagoranci ne na hannu kan kiwon iyaye da abinci na yara.[25]
Rayuwa ta Aure
[gyara sashe | gyara masomin]
A ranar 29 ga watan Yunin 2012, Esha Deol ta auri Bharat Takhtani a wani bikin aure a haikalin ISKCON a Mumbai.[26][27]
A cikin watan Afrilun 2017, an sanar da cewa ma'auratan suna tsammanin ɗansu na farko. Ta haifi 'yarta a watan Oktoban 2017 a asibitin Hinduja da ke Mumbai kuma ta sanya mata suna Radhya.[28] A ranar 10 ga Yunin shekarar 2019, ta haifi 'yarta ta biyu, Miraya.[29] A ranar 6 ga watan Fabrairun 2024 Deol da mijinta Takhtani sun sanar da rabuwa bayan shekaru 12 da aurensu.[30][31]
Harkar Fim
[gyara sashe | gyara masomin]Fim
[gyara sashe | gyara masomin]- Duka fina-finan na Hindi ne, sai dai in an lura wani baya daga ciki sai a sanar ko a gyara.
| Denotes films that have not yet been released |
| Shekara | Suna | Matsayi | Bayanan kula | Madogara |
|---|---|---|---|---|
| 2002 | Koi Mere Dil Se Poochhe | Esha Singh | ||
| Na Tum Jaano Na Hum | Esha Malhotra | [32] | ||
| Kyaa Dil Ne Kahaa | Esha Kapoor | |||
| 2003 | Kucch To Hai | Tanya Oberoi | ||
| Chura Liyaa Hai Tumne | Tina Khanna | |||
| LOC: Kargil | Dimple Cheema | [33] | ||
| 2004 | Aayutha Ezhuthu | Geetanjali | Simultaneously shot in Tamil and Hindi | |
| Yuva | Radhika | |||
| Dhoom | Sheena Rai | credited as Esha | [34] | |
| 2005 | Insan | Heena Khan | credited as Esha | |
| Kaal | Riya Thapar | |||
| Main Aisa Hi Hoon | Maya Trivedi Thakur | credited as Esha | ||
| Dus | Agent Neha (Fake) | |||
| No Entry | Pooja Khanna | [35] | ||
| Shaadi No. 1 | Diya Saxena | |||
| 2006 | Pyare Mohan | Preeti Ahuja | credited as Esha | [36] |
| Ankahee | Kavya Krishna | credited as Esha | ||
| 2007 | Just Married | Ritika "Ritu" Khanna Sachdeva | ||
| Darling | Geeta Menon | |||
| Cash | Pooja | |||
| 2008 | Sunday | Herself | Special appearance in song "Kashmakash" | |
| Money Hai Toh Honey Hai | Herself | Special appearance in song "Ta Na Na" | ||
| One Two Three | Jiya | |||
| Hijack | Saira | |||
| 2011 | Tell Me O Kkhuda | Tanya R. Kapoor | ||
| 2015 | Kill Them Young | Meera | Simultaneously shot in Kannada as Care of Footpath 2 | |
| 2019 | Cakewalk | Shilpa Sen | Short film, credited as Esha Deol Takhtani | [37] |
| 2021 | Ek Duaa | Abida | Short film, credited as Esha Deol Takhtani | [38] |
| 2025 | Tumko Meri Kasam | Meenakshi Sharma | [39] |
Talabijin
[gyara sashe | gyara masomin]| Shekara | Suna | Matsayi | Bayanan kula | Madogara |
|---|---|---|---|---|
| 2015 | Roadies X2 | Gang Leader | Season 12 | [40] |
| 2022 | Rudra: The Edge of Darkness | Shaila "Shai" Durrani Singh | [41] | |
| 2023 | Hunter Tootega Nahi Todega | Divya |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Filmfare Awards: Winners of 2002". The Times of India. Archived from the original on 17 January 2004. Retrieved 6 November 2012.
- ↑ "Esha Deol celebrates birthday with hubby and close friends". Mid-Day. 4 November 2015. Archived from the original on 24 March 2016. Retrieved 30 March 2016.
- ↑ "I want Esha to have a baby soon: Hema Malini". The Indian Express. 2 November 2015. Archived from the original on 11 December 2015. Retrieved 30 March 2016.
- ↑ "The Deols". vijaytafilms. Archived from the original on 6 June 2011. Retrieved 23 September 2011.
- ↑ "My father is a die-hard Punjabi: Esha Deol". Hindustan Times (in Turanci). 7 March 2015. Archived from the original on 16 January 2020. Retrieved 16 January 2020.
- ↑ "Happy Birthday Hema Malini: As original dream girl turns 71, see her family pics with Dharmendra, Esha Deol". Hindustan Times (in Turanci). 16 October 2019. Archived from the original on 13 January 2020. Retrieved 16 January 2020.
- ↑ Pradhan, Bharathi S. (24 June 2012). "Esha Deol's big fat wedding". The Telegraph (India) (in Turanci). Archived from the original on 16 January 2020. Retrieved 16 January 2020.
- ↑ Syed Firdaus Ashraf (19 May 2004). "I am today's woman: Esha Deol". Rediff.com. Archived from the original on 10 October 2016. Retrieved 16 January 2020.
- ↑ Savera R Someshwar (11 January 2002). "Can Esha act?". Rediff. Archived from the original on 26 April 2017. Retrieved 6 November 2012.
- ↑ Rakesh Budhu. "Koi Mere Dil Se Pooche Review". Planet Bollywood. Archived from the original on 26 April 2017. Retrieved 6 November 2012.
- ↑ Taran Adarsh (24 January 2003). "Kucch To Hai Review". IndiaFm. Archived from the original on 20 September 2015. Retrieved 17 December 2012.
- ↑ Taran Adarsh (24 March 2003). "Chura Liyaa Hai Tumne Review". IndiaFm. Archived from the original on 20 October 2012. Retrieved 17 December 2012.
- ↑ Taran Adarsh (25 December 2003). "Loc-Kargil Review". IndiaFm. Archived from the original on 8 April 2016. Retrieved 17 December 2012.
- ↑ Anita Bora (25 December 2003). "Why we can never forget Kargil". Rediff. Archived from the original on 19 February 2013. Retrieved 17 December 2012.
- ↑ "Top Earners: Box Office 2003". Box Office India. Archived from the original on 25 May 2012. Retrieved 17 December 2012.
- ↑ "Movie Review: Aayitha Ezhuthu". Sify. Archived from the original on 26 September 2013. Retrieved 17 December 2012.
- ↑ "'I am today's woman – very independent, very bindaas'". Rediff. 19 May 2004. Archived from the original on 17 May 2013. Retrieved 17 December 2012.
- 1 2 "Top Earners: Box Office 2004". Box Office India. Archived from the original on 7 January 2013. Retrieved 17 December 2012.
- ↑ "IIFA : IIFA Awards – Past Awards – IIFA 2004 – Introduction". Archived from the original on 8 June 2010. Retrieved 6 July 2012.
- ↑ Sawhney, Anubha (5 January 2002). "Of Esha & the Deol within". The Times of India. Archived from the original on 23 February 2023. Retrieved 23 February 2022.
- ↑ Samir Gill, Anusha (8 January 2002). "My Dream Debut". Rediff. Archived from the original on 24 April 2003. Retrieved 23 February 2022.
- ↑ "When Hema Malini stood up against Dharmendra after he asked Esha and Ahana to not learn dance". Hindustan Times. 16 October 2021. Archived from the original on 18 July 2023. Retrieved 18 July 2023.
- ↑ Basu, Nilanjana (21 August 2018). "When Little Esha And Ahana Deol Danced With Mom Hema Malini. See Throwback Pic". NDTV. Archived from the original on 12 August 2023. Retrieved 18 July 2023.
- ↑ "Esha Deol announces her first book 'Amma Mia' based on parenting- a subject which is very close to her heart". The Times of India. 10 February 2020. Archived from the original on 12 October 2020. Retrieved 24 March 2020.
- ↑ "Esha Deol Takhtani shares her baby care tips with 'Amma Mia'". The New Indian Express. 24 March 2020. Archived from the original on 24 March 2020. Retrieved 24 March 2020.
- ↑ "Esha Deol to wed in temple on June 29". The Indian Express. Mumbai. 11 June 2012. Archived from the original on 6 January 2013. Retrieved 11 June 2012.
- ↑ Jha, Subhash K (11 June 2012). "Esha Deol to wed in a temple". The Times of India. Archived from the original on 29 July 2021. Retrieved 4 May 2022.
- ↑ "Hema Malini's daughter Esha Deol pregnant with her first child". The Times of India. 2017. Archived from the original on 10 September 2018. Retrieved 25 November 2018.
- ↑ "Esha Deol blessed with a baby girl!". The Times of India (in Turanci). 11 June 2019. Archived from the original on 12 June 2019. Retrieved 12 June 2019.
- ↑ Verma, Sakshi (6 February 2024). "Esha Deol, Bharat Takhtani confirm separation after 12 years of marriage". India TV News. Retrieved 6 February 2024.
- ↑ "Esha Deol opens up on being a single parent after divorce with Bharat Takhtani: 'Let the children not suffer, be that one unit'". The Indian Express. 19 March 2025. Retrieved 28 April 2025.
- ↑ "God knows Na Tum Jaano Na Hum is excellent". BBC. 24 September 2014. Archived from the original on 29 April 2022. Retrieved 5 May 2022.
- ↑ "LOC-Kagil: How 'real'?". The Hindu. 18 January 2004. Archived from the original on 14 January 2005. Retrieved 10 August 2023.
- ↑ Ashraf, Syed Firdaus (26 August 2004). "People will love Dhoom!". Rediff.com. Archived from the original on 28 October 2021. Retrieved 22 August 2020.
- ↑ "No Entry is no remake of Masti". Bollywood Hungama. 6 October 2004. Archived from the original on 22 February 2014. Retrieved 17 June 2012.
- ↑ "Esha Deol slapped Amrita Rao on the sets of Pyare Mohan: 'I have no regrets because she totally deserved it'". Indian Express. 27 May 2022. Archived from the original on 27 May 2022. Retrieved 27 May 2022.
- ↑ Vasudevan, Aishwarya (16 March 2021). "Esha Deol Takhtani is back to her 'toned self', talks about her comeback in films". DNA India (in Turanci). Archived from the original on 22 March 2021. Retrieved 29 March 2021.
- ↑ Roy Choudhury, Rishita (15 July 2021). "Esha Deol unveils first look of Ek Duaa, film to premiere on Voot Select on July 26". India Today. Archived from the original on 16 July 2021. Retrieved 21 July 2021.
- ↑ "Anupam Kher, Esha Deol wrap up Vikram Bhatt's film 'Tumko Meri Kasam'". ANI News. 10 January 2025. Archived from the original on 15 January 2025. Retrieved 5 March 2025.
- ↑ "MTV Roadies X2 – The ride is smoother!". The Indian Express. Archived from the original on 16 January 2014. Retrieved 22 November 2013.
- ↑ "Esha Deol to make her digital debut with Ajay Devgn-starrer web series Rudra". India Today. 7 July 2021. Archived from the original on 6 October 2021. Retrieved 6 October 2021.
Adireshin Waje
[gyara sashe | gyara masomin]| Wikimedia Commons has media related to Esha Deol. |
- Muƙaloli masu kyau
- CS1 Turanci-language sources (en)
- No local image but image on Wikidata
- Commons category link from Wikidata
- Wikipedia articles with faulty ICCU identifiers
- Pages with red-linked authority control categories
- Wikipedia articles with ISNI identifiers
- Wikipedia articles with LCCN identifiers
- Wikipedia articles with Trove identifiers
- Wikipedia articles with VIAF identifiers
- Wikipedia articles with WorldCat-VIAF identifiers
- Yar fim ta ƙasar Indiya
- Yar fim
- Mata Yan Kwallon na Indiya
- Rayayyun mutane
- Haifaffun 1981