Jump to content

Ethan Mbappé

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ethan Mbappé
Rayuwa
Haihuwa Montreuil (mul) Fassara, 29 Disamba 2006 (17 shekaru)
ƙasa Faransa
Kameru
Ƴan uwa
Mahaifi Wilfrid Mbappé
Mahaifiya Fayza Lamari
Ahali Kylian Mbappé
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Paris Saint-Germain2021-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Ethan Mbappé Lottin (an haife shi ranar 29 ga watan Disamba na shekarar 2006) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Faransa wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta ligue 1 wato Paris Saint-Germain .

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi ne a Montreuil, Seine-Saint-Denis, Mbappé ya girma a cikin dangin ƙwallon ƙafa, tare da ɗan'uwansa Kylian da ɗan'uwa mai suna Jirès Kembo Ekoko dukan su sun kasance ƙwararrun 'yan wasan ƙwallon ƙafa. Mahaifinsu dan kasar Kamaru ne mahaifiyarsu kuma 'yar kasar Aljeriya.

Aikin kungiya

[gyara sashe | gyara masomin]

Ethan ya bi sawun manyan 'yan uwansa ta hanyar shiga cikin kungiyar AS Bondy a shekarar 2015. Bayan shekaru biyu tare da AS Bondy, Mbappé ya koma kungiyar kawallon kafa ta Paris Saint-Germain (PSG) a cikin shekarar 2017, a cikin kasuwar musayar 'yan wasa guda daya da kungiyar din ya kawo dan uwansa Kylian a matsayin aro. [1] Ya zura kwallo a wasansa na farko a kungiyar 'yan kasa da shekaru 12.

Mbappé ya sanya hannu kan sabon kwantiragin shekaru uku da kungiyar kwallon kafa ta PSG ne a watanYuninn shekarar 2021. A ranar 16 ga watan Disamba a shekarar 2022, yana da shekaru 15 a duniya ne, ya fara halartan sa tare da manyan kungiyar a wasan sada zumunci da suka doke Paris FC da ci 2–1.

Ayyukan kasa da kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

An kira Mbappé zuwa tawagar 'yan kasa da shekaru 16 na Faransa a watan Nuwamba 2021.

Ba kamar ɗan'uwansa Kylian ba, dan wasan gaba wanda aka sani da saurin walƙiya, Ethan ɗan wasan tsakiya ne na bangaren hagu.

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Janairun shekarar 2022, Mbappé ya shiga wani dan karamin hatsarin mota, bayan da wani direban bugu ya taka motar da yake ciki. Amma Bai samu wani babban rauni ba.

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named pf

a b c d Ethan Mbappé at the French Football Federation (in French) 2. ^ Spencer, Jamie (17 September 2019). "Who is Ethan Mbappe? Kylian's younger brother in PSG's academy" . 90min . Retrieved 23 February 2022. 3. ^ Johnson, Jonathan (24 February 2018). "Mbappe hits back at Assou-Ekotto criticism" . ESPN . Retrieved 17 April 2022. 4. ^ a b Whiley, Matt (7 February 2022). "Who is Ethan Mbappe and could he be even better than his brother Kylian?" . Planet Sport . Retrieved 23 February 2022. 5. ^ Abayomi, Tosin (30 March 2018). "Brother of PSG star scores on his debut" . Pulse Nigeria . Retrieved 17 April 2022.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]