Jump to content

Falilat Ogunkoya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Falilat Ogunkoya
Rayuwa
Haihuwa Ogun, 5 Disamba 1968 (55 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Mississippi State University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Sport disciplines sprinting (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 
Nauyi 66 kg
Tsayi 172 cm

Falilat Ogunkoya (an haife ta 5 ga watan Disamba shekara ta alib 1968 a Ode Lemo, Jihar Ogun Nigeria ) [1] tsohuwar ƴar wasan tsere ce a Najeriya .

Ogunkoya ta lashe gasar zakarun ƙasa da dama, ciki har da lambar zinare a shekara ta alib 1996 a mita 400, zinari a mita 200 da 400 a shekara ta alib 1998, da kuma zinare a a shekara ta alib 1999 da 2001 a mita 400. A Wasannin shekara ta alib 1987 na Duk Afirka a Nairobi ta sami lambar azurfa a cikin 200 m. A shekara ta alib 1995 a wasannin All Africa a Harare ta lashe azurfa a mita 400, sannan a Wasannin shekarar 1999 a Johannesburg ta sami lambar zinare a mita 400.

A Gasar Olympics ta lokacin bazara ta shekarar 1996 ta ci tagulla a tseren mita 400, a bayan Marie-José Pérec ta Faransa da Cathy Freeman ta Ostiraliya, a matsayin gwarzo mafi kyau da tarihin Afirka na 49.10, wanda a yanzu ita ce ta goma sha biyu mafi sauri a kowane lokaci.

Shekara Gasa Wuri Matsayi Taron Bayanan kula
Representing  Nijeriya
1986 World Junior Championships Athens, Greece 1st 200m 23.11 (wind: +0.6 m/s)
3rd 4 × 100 m relay 44.13
1987 All-Africa Games Nairobi, Kenya 2nd 100 m 11.43
2nd 200 m 22.95
  1. Biography. Official website. Retrieved on 2014-01-12.