Jump to content

Fasfo na Chadi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fasfo na Ƙasar Chadi
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na passport (en) Fassara
Ƙasa Cadi

Ana ba da Fasfo na Chadi ga 'yan ƙasar na Chadi don tafiye-tafiye a ƙasashe waje. An rubuta fasfo na Chadi a cikin sigar harsuna uku; Faransanci, Turanci da Larabci.

Ya zuwa 1 ga watan Janairun 2017, ƴan ƙasar Chadi suna da biza kyuata a wasu ƙasashe da yankuna 51, har-wayau an jera fasfon ƙasar a matsayin na 85 dangane da fasfon da ke bayar da damar yancin tafiye-tafiye (wanda aka haɗa da fasfo na Bhutanese, Sinanci, Mali da Rwanda) bisa ga madogarar (Henley visa restrictions index).[1]

A ranar 24 ga watan Satumba 2017, an dakatar da 'yan kasar Chadi da ke da fasfo na Chadi daga shiga Amurka. Dalilin shi ne cewa hukumomin Chadi sun ƙarar da takardar fasfo da da ake baiwa yan ƙasar kuma ba su iya gabatar da samfurin fasfon ba ga hukumomin Amurkan.[2]

  1. "Global Ranking - Visa Restriction Index 2017" (PDF). Henley & Partners. Archived from the original (PDF) on 8 August 2019. Retrieved 14 March 2017.
  2. Keating, Joshua (19 October 2017). "Finally, We Learn Why Chad Is on the Travel Ban List. It's Not Good". Slate. Retrieved 21 October 2017.