Faski(kauye)

Faski kauye ne dayake karkashin karamar Hukumar baure ta Jihar katsina. Mutanen faski gauraye ne na hausawa da fulani,Kuma dukansu Suna magana da yaren hausa Kuma sunayin bukuwan al'asunau irin na hausawa.[1]
Samuwarsa
[gyara sashe | gyara masomin]Ankafa garin faski a karkashin karamar Hukumar baure shekaru 80 da suka wuce tun kafin zuwan siyasa a ƙasar nigeiya,inda Mai mulkin garin alhaji mohammadu ya gaji sarautar a Wajen kakaninsa
Sana'arsu
[gyara sashe | gyara masomin]Mutanen faski Mafi yawansu manomane Kuma makiyaya ne inda suke noma duk wani na'in abinchi na hausawa.
Abubuwan da suke nomawa
[gyara sashe | gyara masomin]Abubuwan da Mutanen faski suke nomawa sun shafi gero,dawa,masara,wake da Kuma sauran kayan masarufi.
Yanayin garin
[gyara sashe | gyara masomin]Garin ne Mai dadin Zama Wanda yake karkashin karamar Hukumar baure wace takeda girman kasa da yakai kimanin 707Km². Kauyen faska yanada yanayin zafi ko sanyi da yakai kimanin 36C.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.11. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.11. ISBN 978-2105-93-7.