Jump to content

Fatou Mass Jobe-Njie

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fatou Mass Jobe-Njie
ambassador (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Serekunda (en) Fassara, 20 century
ƙasa Gambiya
Karatu
Makaranta University of Wolverhampton (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya da minista

Fatou Mass Jobe-Njie 'yar siyasa ce 'yar ƙasar Gambiya wacce ta riƙe muƙamin ministar yawon buɗe ido da al'adu daga shekarun 2010 zuwa 2014 da jakadiya a Malaysia daga shekarun 2014 zuwa 2015.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Jobe-Njie daga Serekunda take. Mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama kuma mahaifiyarta ta rasu bayan ’yan shekaru. Jobe-Njie da ƴan uwanta kawunsu ne ya rene su. [1] Ta halarci Makarantar Firamare ta Serre-Kunda da Sakandare na St. Joseph. [2]

Jobe-Njie tana da MBA daga Jami'ar Wolverhampton. [3]

Jobe-Njie ta yi aiki a kamfanoni masu zaman kansu kuma ta shugabanci sashen tallace-tallace a bankin Standard Chartered, kafin ta jagoranci harkokin banki na PHB. [3] [4] Ta kuma yi aiki a matsayin shugabar kungiyar agaji ta Red Cross ta Gambia kuma a watan Mayun 2010 aka zaɓe ta shugabar kungiyar tafiye-tafiye ta Afirka. [5] [6]

Shugaba Yahya Jammeh ne ya naɗa Jobe-Njie ministar yawon buɗe ido da al'adu a ranar 4 ga watan Fabrairun 2010, inda ta maye gurbin Nancy Njie. [7] A cikin shekarar 2013, ta sa ido kan kafa kungiyar tattarawa ta Gambia don tattarawa da rarraba kuɗaɗen sarauta ga masu fasahar Gambia a ƙarƙashin dokar haƙƙin mallaka. [8] A watan Yunin 2014, ta gabatar da jawabi a taron ƙasa da ƙasa na OIC kan rawar da ta taka na yawon buɗe ido na Musulunci ke takawa a tattalin arzikin duniya.[9] A watan Satumban 2014 ne Jammeh ya kore ta, ba tare da bayyana wani dalili ba. [3] Bayan kwana biyu, an naɗa ta a matsayin jakadiyar Gambia a Malaysia, wakiliyar dindindin ta farko a ƙasar. [4] [10] [11] Mataimakin ta Abubacarr Jah ya maye gurbinta a cikin watan Mayu 2015. [12]

Jobe-Njie ta koma Gambiya kuma ta zama mataimakiyar Zeinab Jammeh kuma babban darektan kungiyar agaji ta Jammeh, Operation Save the Children Foundation. [13] [14]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Jobe-Njie ta auri Farfesan Jami’ar Gumbo Tournay, wanda bayan shekaru da dama aka wanke shi da laifin bayar da bayanan karya ga ofishin shugaban ƙasa bayan ya yi magana game da cin hanci da rashawa a Jami’ar Gambia. [15] [16] Sun haifi ɗansu Ousman a lokacin da suke zaune a Landan. [17] Bayan rabuwarsu, Jobe-Njie ta auri maigidan otal mai suna Buna Njie. [18]

  1. "Gambia: Chief Jammeh Enabler Fatou Mass Is A Close Relative Of The IEC Chairman!". Freedom Newspaper. 24 October 2016. Archived from the original on 27 October 2016. Retrieved 3 February 2017.CS1 maint: unfit url (link)
  2. Jallow, Hassan (29 May 2016). "Gambian Brains: The Best and Brightest from St. Joseph's High". Daily Observer. Retrieved 3 February 2017.
  3. 3.0 3.1 3.2 "Gambia's Tourism Minister Removed". Jollof Media Network. 13 September 2014. Archived from the original on 25 December 2018. Retrieved 3 February 2017. Cite error: Invalid <ref> tag; name "sacked" defined multiple times with different content
  4. 4.0 4.1 "Sacked Gambian Tourism Minister Named Ambassador". Jollof Media Network. 15 September 2014. Archived from the original on 24 December 2018. Retrieved 3 February 2017. Cite error: Invalid <ref> tag; name "named" defined multiple times with different content
  5. "Gambia Minister of Tourism and Culture named new ATA president". ETN. 25 May 2010. Retrieved 3 February 2017.
  6. Ansu Manneh, Kebba (26 May 2010). "Fatou Mass Jobe-Njie elected as president of ATA's Board of Directors". Today. Archived from the original on 25 August 2010. Retrieved 3 February 2017.
  7. "Jammeh sacks four ministers, appoints six". The Point. 9 February 2010. Retrieved 3 February 2017.
  8. "Gambia: The Gambia Royalty Collecting Society Inaugurated By Minister Jobe-Njie". All Africa. 3 May 2013. Archived from the original on 4 February 2017. Retrieved 3 February 2017.
  9. Jobe-Njie, Fatou Mass (9 June 2014). "The role of Islamic tourism in the global economy". Travel Impact Newswire (Press release). Retrieved 3 February 2017.
  10. Nyockeh, Abdoulie (15 September 2014). "Gambia: Fatou Mass Jobe-Njie Is New Ambassador to Malaysia". All Africa. Retrieved 3 February 2017.
  11. Saliu, Yunus S. (23 October 2014). "Gambia: KM Bids Ambassador 'Fatou Mass' Farewell". The Daily Observer Banjul. All Africa. Retrieved 3 February 2017.
  12. "Changes in diplomatic circles". The Point. 18 May 2015. Retrieved 3 February 2017.
  13. "First Lady gives gifts to 1st born babies". Republic of the Gambia Office of the President. 10 January 2017. Archived from the original on 25 July 2017. Retrieved 3 February 2017.
  14. Phatey, Sam (31 October 2016). "Aide to Gambia's first lady said Jordanian princess pledged half a million dollars to her foundation". SMBC News. Retrieved 3 February 2017.
  15. Sowe, Fatou (19 July 2012). "Gambia: Gumbo Touray Opens Defence". Daily Observer Banjul. All Africa. Retrieved 3 February 2017.
  16. Sameteh, Bakary (5 October 2012). "Gumbo Ali Touray freed at last". The Point. Retrieved 3 February 2017.
  17. "Amie Dibba and Ous CEO Touray tied the nut. Will the wedding take place in The Gambia, the US or UK?". Gambia Talents Promotion. 29 April 2014. Archived from the original on 26 December 2018. Retrieved 3 February 2017.
  18. "Gambia: Fatou Mass Jobe Has Sold Her Soul To The Jammehs!". Freedom Newspaper. 22 October 2016. Archived from the original on 23 October 2016. Retrieved 3 February 2017.CS1 maint: unfit url (link)