Fatoumata Kaba
| Fatoumata Kaba | |
|---|---|
Fatoumata Lejeune-Kaba | |
| Haihuwa | 1969 |
| Dan kasan | Guinea |
| Aiki | Journalist |
Fatoumata Lejeune-Kaba (an haife ta a shekara ta 1969 [1] ) 'yar jarida ce ta Guinea wacce ke aiki da UNHCR a matsayin Jami'ar Sadarwa.
Kaba ta yi karatu a Amurka, inda ta halarci makarantar sakandare ta Woodrow Wilson da Kwalejin Montgomery da ke Maryland kuma ta kammala karatun digiri a aikin jarida. Ta koma Guinea a shekarar 1992, inda ta yi aiki a gidan rediyo da talabijin na kasar Guinea da CNN a shekarar 1998, ta zama wakiliyar kamfanin dillancin labarai na Reuters . Daga baya, ta yi aiki da Sashen Sadarwa na Shirin Ci Gaban Majalisar Dinkin Duniya kafin ta shiga Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) a 2000. [1]
A ranar 25 ga Fabrairu, 2002, an nada Kaba a matsayin wakiliyar UNHCR na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Jamhuriyar Kongo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Gabon, Kamaru, da Uganda ; ta kasance a Kinshasa . [1] Ta kuma kasance a Ivory Coast ko Cote d'Ivoire bayan haka. A halin yanzu tana Geneva a matsayin jami'ar sadarwa mai kula da Tsakiya, Gabas, Yamma da Kudancin Afirka da Kididdiga.
Magana
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 "Fatoumata Kaba.", Jeuneafrique.com, March 4, 2002 (in French).