Fenerbahçe S.K.
|
| |
| Bayanai | |
| Gajeren suna | FB da Fener |
| Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
| Ƙasa | Turkiyya |
| Aiki | |
| Mamba na |
European Football Clubs (en) |
| Bangare na |
Fenerbahçe SK (en) |
| Mulki | |
| Shugaba |
Aziz Yıldırım (mul) |
| Hedkwata |
Kadıköy (mul) |
| Sponsor (en) | Turkish Airlines |
| Tarihi | |
| Ƙirƙira | 1907 |
|
| |

Fenerbahçe Spor Kulübü (furuci a Turkiya: [feˈnæɾbahtʃe spoɾ kuˈlyby], Kungiyar Kwallon Kafa ta Fenerbahçe) wata babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce da ke cikin ƙasar Turkiyya, wadda aka kafa a shekara ta 1907 a birnin Istanbul. Ƙungiyar na daga cikin manyan kungiyoyi uku mafi shahara a ƙasar, tare da Galatasaray da Beşiktaş, kuma ta lashe Kofin Zakarun Kasar Turkiya har sau 28,[1][2][3] tare da lashe Kofin Kasa har sau shida, Kofin Zakarun Kwallon Kafa na Turkiya (sau uku) da kuma Süper Lig (sau 19).[4] An fi saninta da suna "Sarı Kanaryalar", ma’ana tsuntsayen rawaya, saboda launin rigarta.[5]
Fenerbahçe tana buga wasanninta na gida a filin wasa na Şükrü Saracoğlu Stadium wanda ke cikin yankin Kadıköy na Istanbul. Filin wasan na ɗaukar dubban magoya baya kuma yana daga cikin manyan filayen wasa a Turkiyya.[6]
Ƙungiyar ta samu nasarori da dama a gasar Süper Lig (babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Turkiyya), inda ta lashe kofin lig sau da dama tun bayan kafuwarta. Haka kuma, ta yi fice a gasar Turai kamar UEFA Europa League da UEFA Champions League, duk da cewa ba ta taɓa lashe Champions League ba.[7]
Fenerbahçe na da babbar kishiya da ƙungiyar Galatasaray, inda wasansu ake kira Intercontinental Derby, wanda yake ɗaya daga cikin manyan wasannin ƙwallon ƙafa mafi zafi a duniya. Wannan wasa yana jan hankalin miliyoyin magoya baya a Turkiyya da ma duniya baki ɗaya.[8]
Ƙungiyar ta kuma taka rawa sosai wajen haɓaka matasa 'yan wasa, inda take da makarantar horas da 'yan ƙwallo (academy) da ta samar da fitattun 'yan wasa da dama. Wasu daga cikin fitattun 'yan wasan da suka taka leda a Fenerbahçe sun haɗa da Alex de Souza da Robin van Persie.[9]
Baya ga ƙwallon ƙafa, Fenerbahçe ƙungiya ce mai sassa da dama, ciki har da kwando (basketball), wasan tennis, da sauran wasanni, wanda ya sa take daga cikin manyan kungiyoyin wasanni a Turkiyya baki ɗaya.[10]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "FENERBAHÇE (FB) TOPLAM ŞAMPİYONLUK SAYISI". Hürriyet (in Harshen Turkiyya). 2023. Retrieved 23 May 2024.
... Fenerbahçe, toplamda 28 Türkiye şampiyonluğu ile en çok şampiyon olan Türk futbol takımıdır. Süper Lig'de 19 kez, Millî Küme'de 6, Türkiye Futbol Şampiyonası'nda ise 3 kez birinci olarak Türk futbol tarihinde en çok millî şampiyonluk yaşamış takımdır ...'
- ↑ "Fenerbahçe Spor Kulübü 116 yaşında". Anadolu Ajansı (in Harshen Turkiyya). 3 April 2023. Retrieved 23 May 2024.
... Futboldaki başarılar – Sarı-lacivertliler, 19'u Süper Lig, 6'sı Milli Küme ve 3'ü Türkiye Futbol Şampiyonası adı altında toplamda 28 kez Türkiye Şampiyonu oldu. ...'
- ↑ "Fenerbahçe en son ne zaman şampiyon oldu? Fenerbahçe kaç kere şampiyon oldu?". haberler.com (in Harshen Turkiyya). 5 May 2025. Retrieved 18 May 2025.
... Fenerbahçe: 28 ... Galatasary: 25 ...'
- ↑ "Turkcell Süper Kupa 2025 — Page 12-13". TFF.org (Online Magazine) (in Harshen Turkiyya). 2025. Retrieved 15 March 2026.
Fenerbahçe Tarihi — Şampiyonlukları: ♦ Türkiye Futbol Birinciliği (1924–1951) 3 defa ♦ Millî Küme (1937–1950) 6 defa ♦ Türkiye Ligi (1959–...) 19 defa
- ↑ Fenerbahçe Official History
- ↑ Stadium Guide Turkey
- ↑ UEFA Club Records
- ↑ Football Rivalries Report
- ↑ Fenerbahce Player Archive
- ↑ Fenerbahce Sports Club Overview