Jump to content

Firinji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
firinji
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na major appliance (en) Fassara, chiller (en) Fassara, home appliance (en) Fassara da electrical appliance (en) Fassara
Amfani refrigeration (en) Fassara, food storage (en) Fassara da food preservation (en) Fassara
Wanda yake bi ice house (en) Fassara, cooler (en) Fassara da icebox (en) Fassara
Time of discovery or invention (en) Fassara 1856
Uses (en) Fassara refrigerant (en) Fassara
MCN code (en) Fassara 8704.32.30
wajen Aje kayan sanhi

Firinji dai wata na'ura ce mai daɗaɗɗen tarihi da ake amfani da ita wajen ajiye kayayyakin abinci, ko maganin da yanayin zafi kan iya lala tawa. Kuma a kan yi ajiyar ruwa a cikin sa domin ya sanyaya. Amma dai ko kafin ƙirƙirar firinji, an yi amannar cewa, mutanen da can na da dabaru irin nasu na adana abinci ba tare da ya lalace ba.Kuma irin waɗannan dabaru ne sannu a hankali aka inganta,har firinji ya samu da yanzu ake amfani da shi a gidaje da kuma dakunan girki irin na zamani. Tsayayyen yanayi da akafi ajiye kayan abinci shine 3 - 5 °C (37 - 41 °F).[1]

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

Mutanen da, kamar yadda bincike ya nuna sukan sami wuri mai sanyi kamar gaɓar kogi su adana abinci don kar ya lalace, ko kuma su haƙa ƙarƙashin ƙasa a wuri mai dausayi. A ƙasahen da tsabar yanayin hunturu kan sanya zubar dusar ƙanƙara kuwa, tun kafin ƙarni na 19 mutane kan sari dunƙulen ƙanƙarar su saka cikin wani ɗan akwatin katako, kana su jera nau'o'in abincin da ke buƙatar sanyi don kar su lalace.

Irin waɗannan dabaru ne dai masu bincike irin su Dr. William Cullen da Dr. John Goorie da Michael Faraday, suka gina fasahar su akai, tun a farkon ƙarni na 18 da tunanin samar da wata na'urar sanyi da tafi wancan akwatin katako na kankara inganci.

Waɗannan dabarun masu bincike ne dai wani Bajamushe mai suna Injiniya Carl Von Linden, ya tattara a shekarar ta alif 1876, ya ƙera firinji na farko a duniyar nan. Inda Injiniya Linden ya ci gaba da bincike tare da inganta wannan fasaha tasa ta ƙera firinji. Sauran masana da kuma injiniyoyi na wannan zamani kuma suka kwaikwayi fasahar Injiniya Linden suka ci gaba da ƙera firinji.

Firinji

Ya zuwa shekara ta alif 1920 dai, an samu kafuwar kamfanoni fiye da 200 da suke ƙera firinji iri daban-daban a wannan duniya, bisa dogaro da fasahar Injiniya Linden, wanda aka yi ittifaƙin cewar shi ne ya fara ƙirkirar firinji har 'yan baya suka runguma.

Ire-iren Firinji[gyara sashe | gyara masomin]

Amfanin Firinji[gyara sashe | gyara masomin]

Adana abinci kar ya lalace. `

Yaɗuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Yau dai an wayi gari cewar, firinji ya zama ruwan dare game duniya. Ya kuma zama wani sinadari na tafiyar da rayuwa, kama daga amfani da shi wurin adana abinci zuwa samar da ƙanƙara, kai har ma da killace magani walau na Bature ko kuma na gargajiya, domin kare shi daga lalacewa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. . Keep your fridge-freezer clean and ice-free. BBC. 30 April 2008