Jump to content

Florence Kabugho

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Florence Kabugho
member of parliament (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Uganda, 
ƙasa Uganda
Sana'a
Sana'a ɗan jarida da radio journalist (en) Fassara

Florence Kabugho 'yar siyasar ƙasar Uganda ce kuma tsohuwar 'yar jarida ta rediyo, wacce aka zaɓa a majalisar dokoki ta goma sha ɗaya ta Uganda a babban zaɓen shekara ta 2021, a matsayin wakiliyar gundumar Kasese mace. [1][2][3]

Kafin shiga siyasa Florence 'yar jarida ce ta gidan rediyo. Ta yi murabus daga aiki a gidan rediyon Uganda don yin aiki a gidan rediyon Meshia FM da ke yankin Rwenzori.[4] Ta yi aiki da Omusinga Charles Mumbere na Rwenzururu, a ayyuka da yawa, ciki har da Mataimakinyar Kakakin Masarautar, Ministan Jinsi da Ministar Sadarwa. Lokacin da aka kai hari a fadar kuma aka kama Mumbere a shekarar 2016 ta kusan rasa ranta. [5]

A watan Yulin 2020 Winnie Kiiza ta sanar da yin murabus daga harkokin siyasa, bayan shekaru goma sha biyar a matsayin 'yar majalisa a gundumar Kasese. Florence Kabugho na ɗaya daga cikin 'yan takara huɗu da za su gaji Kiiza a zaɓen fidda gwani na FDC.[6] Ta samu nasarar lashe zaɓen FDC a zaɓen fidda gwani na FDC na watan Agusta 2020, inda ta samu kuri'u 259 Catherine Muhindo (kiri'u 111), Ruth Kabguho (kiri'u 54) da Annet Night ( kuri'u 39).[7]

hoton Florence Kabugho

A watan Nuwambar 2020 Kabugho na cikin 'yan takarar FDC da 'yan sanda suka hana su kaddamar da takardunsu a wuraren wasan yara a ƙaramar hukumar Karambi.[8] [9] Ta ce abubuwan da ta sa a gaba su ne ilimi ga yara mata da cibiyoyin kiwon lafiya na cikin gida. [10] Bayan da Kizza Besigye ya yanke shawarar kin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekara ta 2021, Kabugho ta yi hasashen cewa jam'iyyar FDC za ta ci gaba da goyon bayan 'yan majalisa a Kasese. [11]

An zaɓi Florence zuwa Majalisa a babban zaɓen shekarar 2021, a matsayin wakiliyar mata na gundumar Kasese. Yayin da jam'iyyar FDC ta rasa wasu kujeru uku a Kasese zuwa NRM, jam'iyyun adawa na cikin gida sun haɗa karfi da karfe don zaɓen kananan hukumomi da na magajin gari. [12]

  1. "Kabugho Florence - 2021 General Election - Visible Polls". visiblepolls.org (in Turanci). Retrieved 2023-02-09.
  2. "Parliament: 256 MPs Have So Far Taken Oath for New Term". ChimpReports (in Turanci). 2021-05-18. Retrieved 2023-02-09.
  3. Writer, Maurice Muhwezi | REDPEPPER Staff (2021-05-18). "PICTORIAL: MPs Take Oath as Joy, Vigour Open Eleventh Parliament". Redpepper Uganda (in Turanci). Archived from the original on 2023-02-09. Retrieved 2023-02-09.
  4. "Busongora South MP defeated in FDC primaries". The Independent. 4 August 2020. Retrieved 21 February 2021.
  5. Nathan Ngobi; Simon Turibamwe (24 July 2020). "Hot! Battle for Kasese Woman MP seat heats up". The Second Opinion. Retrieved 21 February 2021.
  6. "Kiiza quits elective politics after 15 years as Kasese Woman MP". 14 July 2020. Retrieved 21 February 2021.
  7. "Busongora South MP defeated in FDC primaries". The Independent. 4 August 2020. Retrieved 21 February 2021.
  8. "Busongora South MP defeated in FDC primaries". The Independent. 4 August 2020. Retrieved 21 February 2021.
  9. Basaija Idd (10 November 2020). "Police Blocks FDC Mass Campaign Launch in Kasese". Uganda Radio Network. Retrieved 21 February 2021.
  10. Basaija Idd (13 November 2020). "Female Candidates in Kasese Promise to Improve Education and Maternal Health". Uganda Radio Network. Retrieved 21 February 2021.
  11. Blanshe Musinguzi; Basaija Idd; Kule Jerome Bitswande (14 December 2020). "FDC Still Hopes for Victory in Kasese Even Without "Loved" Besigye"". Uganda Radio Network. Retrieved 21 February 2021.
  12. Basaija Idd (19 January 2021). "Opposition Team Up in Kasese Ahead of LC V, Mayoral Elections". Ugandan Radio Network. Retrieved 21 February 2021.