Franz Beckenbauer
Appearance
Franz Anton Beckenbauer (an haifeshi a ranar 11 ga watan satumba a shekarar 1945 sannan ya mutu ne a ranar 7 ga watan janairu a shekarar 2024) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne, koci, kuma jami'i. Wanda ake yi wa lakabi da der Kaiser "Sarkin Sarki" ana masa kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan 'yan wasa na kowane lokaci, kuma yana daya daga cikin 'yan wasa tara da suka ci Kofin Duniya na FIFA, Kofin Zakarun Turai, da Ballon d'Or.