Funmilayo Olayinka
Funmilayo Olayinka | |||
---|---|---|---|
15 Oktoba 2010 - 6 ga Afirilu, 2013 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ado Ekiti, 20 ga Yuni, 1960 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||
Mutuwa | Lagos,, 6 ga Afirilu, 2013 | ||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Sankara) | ||
Karatu | |||
Makaranta | Central State University (en) | ||
Harsuna |
Yarbanci Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Ma'aikacin banki | ||
Wurin aiki | Jahar Ekiti | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Action Congress of Nigeria |
Olufunmilayo Aduni Olayinka, Mai suna Famuagun (An haife ta a ranar ashirin 20 ga watan Yuni shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin1960 - ta mutu ranar 6 ga watan Afrilun shekarar dubu biyu da sha ukku 2013), ta kasance ma'aikaciyar banki ce a Nijeriya. kuma 'yar siyasa ce wadda ta yi aiki a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar Ekiti. [1][2][3][4]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Olayinka a Ado-Ekiti dake jihar Ekiti.[5] Ta halarci makarantar Holy Trinity Grammar School Ibadan inda ta samu takardar shedar kammala karatun ta na farko da sakamako mai kyau. Daga nan sai ta zarce zuwa makarantar sakandaren Olivet Baptist, a jihar Oyo, Nijeriya inda ta samu takardar shedar kammala makarantar sakandare (HSC)[6] Ta yi digiri na biyu a fannin Gudanar da Jama'a da kuma Kwalejin Kasuwanci daga Jami'ar Jihar ta Tsakiya, Wilberforce, Ohio ta Amurka a shekara ta (1981), zuwa shekara ta (1983), bi da bi.[7] Ta kasance sau uku tana lashe lambar girmamawa ta Dean.
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Olayinka, wata masaniya ce kan harkokin kasuwanci da kuma tsara hikima a fannin kasuwanci da tallata haja a karkashin Bankin First Bank of Nigeria Plc. Ta yi aiki tare da First Bank daga shekara ta (1986). Daga baya kuma ta yi aiki a matsayin Manajan Dangantaka na Asusun Lura a Bankin Access, da rusasshen Kamfanin hada-hadar kasuwanci na Bankin [MBC] da United Bank for Africa PLC (UBA).
A watan Agusta shekarar (2002), ta fara aiki a cikin Kamfanin Sadarwa na Kamfanin, sannan ta cigaba da shugabantar Sashen Harkokin Kasuwanci, Bankin United na Afirka. Daga baya ta zama Shugaban, Manajan Gudanarwa da Harkokin Kasuwanci, wanda hakan ke jagorantar kungiyar dake da alhakin isar da wata sanarwa mai gamsarwa da kuma sake sanya sunan Bankin Hadin Kan na Afirka wanda ya taimaka wajen fitar da dabarun kasuwancin bankin da karin darajar zuwa jimlar hoton.[8]
Olayinka ta kuma kasance Mataimakin Shugaban kungiyar na( 2), na kungiyar Manajan Banki tsakanin shekara ta(2002), da shekara ta (2004).[9]
Olayinka ta taka muhimmiyar rawa a yayin hadewar hadadden bankin United Bank for Africa & Standard Trust inda ta shugabanci karamin kwamiti. Ta kuma yi aiki a matsayin mamba a cikin alakan gungiyar Kwamitin Hulɗa da Media.
Har zuwa lokacin da aka zabe ta a matsayin Mataimakiyar Gwamnan Jihar Ekiti, ta kasance Shugabar Kula da Harkokin Kasuwanci, Ecobank Transatlantic Inc inda ta ke da alhakin sanar da ayyukan bankin ga jama'a, gudanar da hulda da Jama'a da kuma ba da martani ga gudanarwa kamar yadda ya shafi jimillar du
daukar hoton banki. Bugu da kari, ta kuma lura da Bangaren Sabis na Cikin Gida tare da daukar nauyin hada-hada gaba daya na ayyukan gudanarwa ga dukkan bankin.[10]
Zaɓe
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan rikicin zaɓe da aka yi a lokacin zaben Gwamnoni na shekara ta (2007),[11] dan takarar Jam’iyyar PDP, an kaddamar da dan takara Segun Oni a matsayin wanda ya lashe zaben. Inda Olayinka tare da Kayode Fayemi suka nufi kotu don kalubalantar sahihancin sakamakon zaben. A ranar( 14), ga watan Oktoba shekara ta (2010), bayan an kwashe tsawon shekaru uku da rabi ana sake gudanar da zaben da kuma daukaka kara a kotu, Kotun daukaka kara da ke zaune a Ilorin, Jihar Kwara, Najeriya ta kori tsohon Gwamna Segun Oni na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da ayyana Dakta Kayode Fayemi na jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) a matsayin sabon gwamnan jihar Ekiti.[12] Bayan haka an rantsar da Misis Olufunmilayo Olayinka a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar ta Ekiti saboda rawar da take takawa a yanzu a matsayin abokiyar takarar Dakta Kayode Fayemi a lokacin zaben gwamna na shekara ta (2007), Ita ce mace ta biyu a tarihin Jihar Ekiti da ta hau kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar. Ta kasance memba na jam'iyyar Action Congress of Nigeria.[13]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Olayinka ta rasu da yammacin ranar 6, ga watan Afrilun shekara ta 2013, bayan doguwar fama da ta sha da cutar daji kuma an yi jana’izarta a Ado-Ekiti.[14]
Olayinka ta kasance mai bin addinin kiristanci, ta rasu ta bar tsohuwar mahaifiyarta, da kuma mijinta da kuma 'ya'ya uku.[15]
Manazartai
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ekiti.com http://www.ekiti.com/ekitinews/display_search.php?news_id=102845
- ↑ Ekiti.com http://www.ekiti.com/ekitinews/display_search.php?news_id=102845
- ↑ Ariyibi, Gbenga (April 26, 2013). "Body of Funmilayo Olayinka, Ekiti Deputy Gov laid to rest". Vanguard. Retrieved 1 July 2013.
- ↑ "Deputy Governor of Ekiti State Mrs Funmilayo Olayinka Is dead". naij.com. 6 April 2013. Retrieved 1 July 2013.
- ↑ "Biography of Mrs Funmi Olayinka". Government of Ekiti State. Archived from the original on 19 February 2016. Retrieved 1 July 2013.
- ↑ The Nation Newspapers 19/08/2010 http://thenationonlineng.net/web3/editorial/opinion/10149.html[permanent dead link]
- ↑ Admin. "Ekiti State Deputy Governor Bows To Cancer At 52". News of the people. Retrieved 24 January 2019.
- ↑ Admin. "Ekiti Deputy Governor, Olufunmilayo Olayinka, dies at 52". Premium Times. Retrieved 24 January 2019.
- ↑ Admin. "Ekiti Deputy Governor, Olufunmilayo Olayinka, dies at 52". Premium Times. Retrieved 24 January 2019.
- ↑ The Sun Newspapers 5 April 2005 http://www.sunnewsonline.com/webpages/features/womanofthesun/2005/April/05/womanofthesun-05-04-2005-002.htm Archived 19 ga Afirilu, 2005 at the Wayback Machine
- ↑ The Nation 3 May 2009 "Archived copy". Archived from the original on 3 May 2012. Retrieved 2010-10-19.CS1 maint: archived copy as title (link)
- ↑ 234NEXT Newspapers 15 October 2010 "Archived copy". Archived from the original on 18 October 2010. Retrieved 2010-10-19.CS1 maint: archived copy as title (link)
- ↑ The Sun Newspapers Monday 18 October 2010. "Archived copy". Archived from the original on 21 October 2010. Retrieved 2010-10-19.CS1 maint: archived copy as title (link)
- ↑ Gbenga Ariyibi (April 26, 2013). "Body of Funmilayo Olayinka, Ekiti Deputy Gov laid to rest". The Vanguard.
- ↑ Femi Makinde (8 April 2013). "Where is your deputy, Olayinka's mother asks Fayemi". The Punch. Archived from the original on 1 October 2015.
Diddigin bayanai na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from January 2017
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Webarchive template wayback links
- CS1 maint: archived copy as title
- Ƴan siyasan Najeriya
- Mutane daga jihar Ekiti
- Mutuwan 2013
- Yarbawa
- Ma'aikatan banki
- Ƴan Najeriya
- Yan siyasa
- Yarbawa yan siyasa