Gaɓar Yamma
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||
| |||||
Suna saboda | Yamma | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Territory claimed by (en) ![]() | State of Palestine, Isra'ila da Jordan | ||||
Ƴantacciyar ƙasa | State of Palestine | ||||
Babban birni | Ramallah | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 2,881,687 (2017) | ||||
• Yawan mutane | 491.76 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Larabci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na |
State of Palestine, Occupied Palestinian territories (en) ![]() ![]() | ||||
Yawan fili | 5,860 km² | ||||
Coastline (en) ![]() | 40 km | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku |
Dead Sea (en) ![]() ![]() ![]() | ||||
Wuri mafi tsayi |
Mount Nabi Yunis (en) ![]() | ||||
Wuri mafi ƙasa |
Dead Sea (en) ![]() | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Ƙirƙira | 1949 | ||||
Muhimman sha'ani | |||||
Tsarin Siyasa | |||||
• Gwamna | Mahmoud Abbas (29 Oktoba 2004) | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi |
new shekel (en) ![]() | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +970 | ||||
Lamba ta ISO 3166-2 | WBK |

Gaɓar Yamma (Larabci|الضفة الغربية) yanki ne da ke Gabashin Tekun Bahar Rum, tsakanin Kogin Jordan da kuma Isra'ila. Yana daga cikin yankunan da ake rikici a kansu tsakanin Falasdinawa da Isra'ila.[1][2] Wannan yanki yana da mahimmanci ta fuskar siyasa, addini, da tarihi a Gabas ta Tsakiya.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Gaɓar Yamma ta kasance ƙarƙashin ikon Jordan daga 1948 zuwa 1967. A shekarar 1967, bayan Yakin kwanaki shida, Isra'ila ta kwace yankin daga Jordan. Tun daga lokacin, yankin ya kasance ƙarƙashin ikon Isra’ila, kodayake Majalisar Ɗinkin Duniya na kallon shi a matsayin ƙasa mai mamaye.[3]
Babban birane
[gyara sashe | gyara masomin]- Ramallah – Hedikwatar Gwamnatin Rikon Kwarya ta Palasɗinu
- Hebron (Larabci: Al-Khalil) – Birni mai dimbin tarihi ga addinan Musulunci da Yahudanci
- Nablus – Wuri mai tarihi da al’adu
- Bethlehem – An haifi Annabi Isa a nan bisa addinin Kiristanci
- Jericho – Daya daga cikin tsoffin birane da ake ci gaba da rayuwa a cikinsu
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Gaɓar Yamma na cikin muradun kafa Ƙasar Palasɗinu, inda Falasɗinawa ke neman mulki mai cikakken iko. Sai dai Isra’ila na ci gaba da mamaye wasu sassa da kuma gina matsugunan Yahudawa wanda hakan ke kara dagula al’amura.
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]
Gaɓar Yamma na da cibiyoyin ilimi da dama, ciki har da makarantun firamare, sakandire da manyan makarantu. Gwamnatin Rikon Kwarya ta Palasɗinu da hukumomin ƙetare na taimakawa wajen tafiyar da harkokin ilimi a yankin. Har ila yau, akwai jami’o’i masu zaman kansu da na gwamnati da ke bayar da gudunmawa wajen ci gaban ilimi da bincike.
Jerin Jami’o’i a Gaɓar Yamma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jami’ar Birzeit – Wata tsohuwar jami’a da ke kusa da Ramallah, daya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a yankin.
- Jami’ar An-Najah ta kasa da kasa – Ita ce mafi girma a yankin, tana a Nablus.
- Jami’ar Hebron – Tana cikin birnin Hebron, tana da fannonin karatu da dama.
- Jami’ar Al-Quds – Tana a kusa da Birnin Qudus, tana da bangarori da dama na karatun kimiyya da al’umma.
- Jami’ar Kudus ta Buɗe (Al-Quds Open University) – Jami’ar da ke ba da damar karatu daga nesa ga ɗalibai a fadin yankunan Palasɗinu.
Addini da al’adu
[gyara sashe | gyara masomin]Yankin na da matsayi na musamman ga addinan Musulunci, Kiristanci da Yahudanci. Wuraren ibada da tarihi da ke yankin na jawo masu ziyara daga sassa daban-daban na duniya.