Ganiou Soglo
17 ga Yuni, 2007 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | 4 ga Janairu, 1961 (65 shekaru) | ||
| ƙasa | Benin | ||
| Ƴan uwa | |||
| Mahaifi | Nicéphore Soglo | ||
| Mahaifiya | Rosine Soglo | ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Faransanci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa, marubuci da minista | ||
| Muhimman ayyuka |
DIX-SEPT MINUTES POUR VIVRE Bénin : la nuit est longue mais le jour vient (en) | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
Benin Rebirth Party (en) | ||
Ganiou Soglo (an haife shi a watan Nuwamba 4, 1962[1]) ɗan siyasan Benin ne na Jam'iyyar Benin Rebirth Party (RB) wanda ya yi aiki a gwamnati na wani lokaci a matsayin Ministan Al'adu, Karatu, da Inganta Harsuna na ƙasa. Shi ɗan tsohon shugaban ƙasar Nicéphore Soglo ne kuma ɗan'uwan Léhady Soglo.
An haifi Soglo, ɗan ƙaramin ɗan tsohon shugaban ƙasar Nicéphore Soglo da tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar Rosine Vieyra Soglo, a birnin Paris.[1] An zabe shi a matsayin dan takarar jam'iyyar RB a majalisar dokokin kasar Benin a zaben 'yan majalisa na watan Maris na 2003.[2] Daga baya, ya kasance dan takara a zaben shugaban kasa na Maris 2006, yana takara duk da zabin Léhady Soglo a matsayin dan takararta.[3] Ganiou ya lashe kusan kuri'u 5,000, wato kashi 0.17% na kuri'un da aka kada.[4]
A cikin wasanni, Soglo ya jagoranci Sharks na kungiyar kwallon kafa ta Atlantic na wani lokaci.[1]
A cikin gwamnatin shugaba Yayi Boni da aka nada a ranar 17 ga watan Yuni, 2007, an nada Soglo a matsayin ministan matasa, wasanni da nishadi.[5][6][7] Daga nan sai aka mayar da shi mukamin Ministan Al’adu, Karatu da Bunkasa Harsuna na Kasa a ranar 22 ga Oktoba, 2008.[8]
A ranar Juma’a, 5 ga Fabrairu, 2021, an harbe Ganiou Soglo a kirji tare da raunata shi a wani harin kwantan bauna da aka kai kusa da garin Zinvié.[9] Soglo fasinja ne a cikin wata mota da ta taso daga wata gona da ya mallaka a Abomey-Calavi lokacin da aka kai harin.[9] Ya yi jinya a asibitin jami’ar Hubert Maga na kasa, kafin a kai shi kasar Faransa don jinya.[10]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Nouveau gouvernement, formé le 17 juin 2007 à Cotonou", Sonangnon.net (in French).
- ↑ List of deputies elected in the 2003 election Archived ga Yuni, 7, 2007 at the Wayback Machine, Benin government page (in French).
- ↑ "Présidentielle 2006 : les principaux candidats" Archived 2007-09-29 at the Wayback Machine, Afrique Express (in French).
- ↑ Elections in Benin, African Elections Database.
- ↑ "Bénin : composition du nouveau gouvernement soumis à l'avis de l'Assemblée Nationale" Archived 2007-07-18 at the Wayback Machine, Xinhua, June 18, 2007 (in French).
- ↑ Governments of Benin, izf.net (in French).
- ↑ Belly Kpogodo, "Entrée surprise de Galiou Soglo au gouvernement : Les raisons qui ont motivé Yayi" Archived 2007-06-22 at the Wayback Machine, La Nouvelle Tribune (sonangnon.net), June 19, 2007 (in French).
- ↑ "Formation d’un nouveau gouvernement au Bénin", Panapress, October 23, 2008 (in French).
- ↑ 9.0 9.1 Millecamps, Matthieu (2021-02-09). "Attaque contre Ganiou Soglo au Bénin : une enquête et des polémiques". Jeune Afrique. Archived from the original on 2021-03-07. Retrieved 2021-07-28.
- ↑ Millecamps, Matthieu (2021-07-25). "Bénin: décès de Rosine Soglo, ex-première dame devenue femme politique de premier plan". Jeune Afrique. Archived from the original on 2021-07-27. Retrieved 2021-07-27.