Jump to content

Gelanesh Haddis

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gelanesh Haddis
Rayuwa
Haihuwa Gojjam (en) Fassara, 1896
ƙasa Habasha
Mutuwa 1986
Sana'a
Sana'a scholar (en) Fassara, Malami, marubuci da maiwaƙe
Kayan kida murya
Imani
Addini Ethiopian Orthodox Tewahedo Church (en) Fassara

Gelanesh Haddis (1896 - 1986) malama ce kuma mai koyarwa a Cocin Orthodox na Habasha.   An san ta da ƙwarewarta tare da wani nau'i na waka mai wahala da ake kira qene .

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Haddis a Silalo a gundumar Gojjam na Habasha a shekarar 1896.[1] Mahaifinta, Haddis Kinan, gwani ne a wani nau'in waƙoƙin Habasha da ake kira qene.[1] A lokacin da take da shekaru takwas, Haddis ta rasa idanunta.[1] Mahaifinta ya koya mata wakar-qene, wanda hakan sabon abu ne a lokacin saboda jinsin ta[2] da nakasar ta.[2]

Haddis ta fara koyarwa tare da mahaifinta a makarantar da ke Silalo.[3] A lokacin mulkin mallakan Italiya a Habasha, sojojin da suka mamaye garin ne suka kashe mahaifinta.

Bayan rasuwar mahaifinta, Haddis ta cigaba da koyarwa ita kadai kuma sama da dalibai dubu biyu ne ke koyon karatu a wajen ta yayin da take koyarwa. Ta kuma horar da sabbin malamai 150 na kidan qene.[3]

Haddis ta zamo kwararra a wakar gene, kuma ta zamo kwararriyar a cikin sauran nau'ukan wakokin kasar Habasha kamar shayarin andimta.[4] Andimta ya kunshi haddace ayoyin Injila na baya da kuma maimaita su ga masu sauraro. Don samun daman haddace su, dole ne ya zamana cewa malami yana da ilimi mai zurfi a kan Injila.[5] Koda yake, ta hanyar kidan qene ne ake haddace Injila.[6] Ta shahara sosai a wajen amfani da mita na qene.[7] Har ma ana mata lakabi da Homer taa Habasha.[8]

Haddis tayi aure kuma tana da 'ya'ya uku, amma yaro daya ya mutu yana karami.[3]

Abunda ta bari

[gyara sashe | gyara masomin]

Haddis ta karya katangar wariya jinsi ta hanyar zama wakiyar qene, sana'ar da mafi yawanci na maza ne zalla.[9] Don tunawa da ita an gina gidan tarihi a Bahir Dar, a gabar Tafkin Tana, inda baki ke iya tuntuba game da wakokin ta.[3]

Game da Tattaunawar Qene 1
  1. 1 2 3 Akyeampong, Emmanuel Kwaku; Gates, Henry Louis Jr. (2012). Dictionary of African biography. Oxford: Oxford University Press. p. 449. ISBN 978-0-19-538207-5. OCLC 706025122.
  2. 1 2 "Textes etDialogue". j.malliarakis.free.fr. Retrieved 2020-02-07.
  3. 1 2 3 4 Akyeampong, Emmanuel Kwaku; Gates, Henry Louis Jr. (2012). Dictionary of African biography. Oxford: Oxford University Press. p. 449. ISBN 978-0-19-538207-5. OCLC 706025122.
  4. "Amhara Contributions to Ethiopian Civilization | Ethiopian Review - Ethiopian News" (in Turanci). Retrieved 2020-02-07.
  5. Daniel, Seblewengel. "The Role of Women in Bible Translation, the Case of Ethiopia" (in Turanci). Cite journal requires |journal= (help)
  6. "Qene Centers and Ecclesiastical Scholarship".[permanent dead link]
  7. Gebrai, Isaias Haileab (2018). "GEEZ ORAL POETRY [QENIE]: A STYLISTICAL AND THEMATIC ANALYSIS". European Journal of Philosophy, Culture and Religion. 2:1: 5.
  8. Merahi, K. K. (2006). The Meaning of Quine: The River of Life: Commercial Printing : Enterprise, 6.
  9. "Dept. of Ethiopian Language and Literature fetes first female author". www.amu.edu.et. Archived from the original on 2021-09-04. Retrieved 2020-02-07.