Jump to content

Gidan Adana Kayan Tarihi na Denshway

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gidan Adana Kayan Tarihi na Denshway
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaMisra
Governorate of Egypt (en) FassaraMonufia Governorate (en) Fassara
Coordinates 30°36′07″N 30°51′13″E / 30.6019°N 30.8536°E / 30.6019; 30.8536
Map
History and use
Openingga Yuli, 1999

Gidan Kayan Tarihi na Denshway gidan adana kayan gargajiya ne a Al-Minufiyah, Misira, mai nisan kilomita 75 daga arewa maso yammacin birnin Alkahira, wanda aka kafa don tunawa da Lamarurrukan Denshawai.

An kafa Gidan kayan gargajiyan, a watan Yulin 1999, don tunawa da abin da ya faru a Denshawai, wani rikici tsakanin jami'an Sojojin Burtaniya da dakarun Masarawa game da jami'an da ke farautar tsuntsaye jinsin kurciya na cikin ƙasar ta Misira [1] wanda mazauna ƙauyen suke kiwatawa domin abinci. Gidan kayan gargajiyan ya girmama Masarawa bakwai waɗanda Burtaniya ta rataye a ranar 26 ga watan Yuni 1906.[ana buƙatar hujja]

Ra'ayin gidan kayan gargajiyan

[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin assasa gidan kayan gargajiyan, ana fatan da zummar tunatar da ƙauyuka game da tarihin da ya taimaka wajen tsara yankin da kuma samar da Cibiyar al'adu wacce za ta ƙara jawo hankalin masu yawon buɗe ido a yankin.[2]

Fasalin gidan

[gyara sashe | gyara masomin]

Tsarin hasumiyar idan na kama da siffar tsuntsaye jinsin kurciya ƴar Masar, da hakan ke bayyana ko alamta lamarin da ya auku daga Sojojin Burtaniya na farautar jinsin tsuntsayen na kurciya don wasanni a wurin su. Ginin yana da matakai uku, waɗanda aka haɗa su da Matakalai. Gidan kayan gargajiyan akwai zane-zane da siffofi waɗanda ke bayyana labarin abin da ya farun.[2]

  1. "Overview: Denshway Museum: Symbol of Egyptian revolution history". 15 October 2017.
  2. 1 2 Rania Khallaf (1 July 1999). "'Our Way Towards a Better Life'". Al-Ahram Weekly Online. Archived from the original on 15 April 2008. Retrieved 29 May 2008.