Jump to content

Gladys Wanga

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gladys Wanga
Governor of Homa Bay County (en) Fassara

Satumba 2022 -
Member of the National Assembly (en) Fassara

31 ga Augusta, 2017 -
District: Homa Bay County (en) Fassara
Election: 2017 Kenyan general election (en) Fassara
Member of the National Assembly (en) Fassara

Rayuwa
ƙasa Kenya
Karatu
Harsuna Duluo
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Gladys Atieno Wanga (née Nyasuna; an haife ta a ranar 7 ga watan Maris 1981) 'yar siyasa ce ta Kenya wacce ita ce Gwamnan gundumar Homa Bay na yanzu. Ita ce Gwamna mace ta farko daga Yankin Yammacin Ƙasar kuma ɗaya daga cikin gwamnoni mata bakwai da aka zaɓa a lokacin Babban Zaɓen Kenya na shekarar 2022. Ta taɓa yin aiki a matsayin Wakiliyar Mata na Gundumar Homa Bay daga shekarun 2013 zuwa 2022. Tana da aure da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Makamashi da Man Fetur (EPRA), George Wanga. [1]

Tarihi da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Gladys ta girma a cikin dangin siyasa suna bin sawun mahaifinta marigayi John Nyasuna, wanda a wani lokaci ya kasance sanannen kansila a gundumar Kisumu, wacce a lokacin ake kira Lardin Nyanza. [2]

Ta halarci Makarantar Sakandare ta 'Yan Mata ta Kisumu inda a wani lokaci aka dakatar da ita saboda yin zanga-zanga. [3] Ta sami digirinta na farko a fannin Gudanar da Lafiya daga Jami'ar Kenyatta a shekarar 2004 sannan daga baya ta kammala karatunta daga Jami'ar Kenyatta a shekarar 2012 tare da digiri na biyu a fannin Gudanar da Lafiya. A Jami'ar Kenyatta, ita ce mace ta farko da ta shiga kuma ta lashe kujerar zaɓe a matsayin Sakatare Janar na Ƙungiyar Ɗalibai. [4]

A farkon rayuwarta, Wanga ita ce Manajar Shirye-shirye a Hukumar Kenyan Rock Art wacce a da ake kira Trust for Africa Art kafin ta ci gaba da riƙe wannan matsayin a Liverpool VCT Care and Treatment. [4] A shekarar 2013, Wanga ta tsaya takarar kujerar wakiliya ta mata a gundumar Homa Bay inda ta yi nasara. [5] A majalisar dokoki, Wanga ta kasance memba a Kwamitin Ma'aikata da Jin Daɗin Jama'a a Kenya. [4]

A ranar 25 ga watan Agusta 2022, ta gaji Cyprian Awiti a matsayin gwamna na biyu na gundumar Homa Bay.[6]

  1. Agencies for Kenya Online News. "Homa Bay Governor Gladys Wanga's Husband Lands Government Job". Kenya Online News. Archived from the original on 11 February 2025. Retrieved 22 January 2025.
  2. "Gladys Wanga". Mzalendo (in Turanci). Retrieved 2021-01-19.
  3. "Schools 7 Female Governors Attended - Kenyans.co.ke". www.kenyans.co.ke (in Turanci). 2022-08-17. Retrieved 2025-07-09.
  4. 1 2 3 "Hon. Wanga, Gladys Atieno Nyasuna | The Kenyan Parliament Website". www.parliament.go.ke. Cite error: Invalid <ref> tag; name "auto" defined multiple times with different content
  5. Owino, Anthony (2019-06-25). "Find Out What Women Reps Do". Kenyans.co.ke. Retrieved 2024-04-16.
  6. Ochomo, Bertha (25 August 2022). "Karua attends Wanga swearing-in ceremony in Homa Bay". The Star. Retrieved 5 September 2022.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]