Gundumar Ayensuano
|
| |||||
|
| |||||
| Wuri | |||||
| |||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | ||||
| Yankuna na Ghana | Yankin Gabashi | ||||
| Labarin ƙasa | |||||
| Sun raba iyaka da | |||||
Gundumar Ayensuano tana ɗaya daga cikin gundumomi talatin da uku a Yankin Gabas, Ghana . [1] [2] [3] Asalinta ya kasance wani yanki ne na gundumar Suhum-Kraboa-Coaltar mai girma a lokacin a cikin 1988, wacce aka ƙirƙira daga tsohuwar Majalisar gundumar Suhum-Kraboa-Coaltar, har zuwa lokacin da aka raba yankin kudancin gundumar don ƙirƙirar Ayensuano ( gundumar) a ranar 28 ga Yunin shekarar 2012; Don haka aka mayar da ragowar yankin suna zuwa Suhum Municipal District, wanda kuma aka mayar da ita matsayin majalisar gunduma a waccan shekarar. Majalisar gundumar tana kudancin yankin Gabas kuma tana da Coaltar a matsayin babban birninta. Yawan jama'ar gundumar kamar a Disamba 2024 ya tsaya a 98,300.
Wakilin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Gundumar tana da mazaɓar guda ɗaya mai suna, Ayensuano wanda ke da yankuna ashirin da bakwai (27). Gundumar ta kasu kashi uku, Obesua Zone, Anum Apapam Zone da Kraboa-Coaltar Zone.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "New Districts & Nominated DCEs" (PDF). ghanadistricts. Archived from the original (PDF) on 5 March 2013.
- ↑ "All Districts". ghanadistricts. Retrieved 8 June 2018.
- ↑ "Districts of Ghana". statoids. Retrieved 8 June 2018.
- ↑ "Ayensuano – Eastern Regional Official Website". easternregion.gov.gh. Retrieved 14 November 2021.
