Gundumar kudu ta andaman
Appearance
Gundumar South Andaman na ɗaya daga cikin gundumomi uku na Yankin Tarayyar Indiya na Tsibiran Andaman da Nicobar, waɗanda ke cikin Tekun Bengal. Sri Vijaya Puram, wadda ita ce babban birnin Yankin Tarayyar, ita ce kuma hedkwatar gundumar. Faɗin yankin da wannan gunduma ta mamaye ya kai murabba'in kilomita 2,640.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An ƙirƙiri wannan gundumar ne a ranar 18 ga Agusta, 2006, ta hanyar raba yankin Andaman na da.[1]
Ilimin kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Gundumar South Andaman tana da fadin murabba'in kilomita 3,181 (murabba'in mil 1,228), inda ta kunshi tsibirin South Andaman, tsibirin Rutland, tsibirin Little Andaman, tsibirin North Sentinel, tsibirin South Sentinel da kuma tsibiran Ritchie's Archipelago.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Law, Gwillim (2011-09-25). "Districts of India". Statoids. Retrieved 2011-10-11.
- ↑ Srivastava, Dayawanti, ed. (2010). "States and Union Territories: Andaman Islands: Government". India 2010: A Reference Annual (54th ed.). New Delhi, India: Additional Director General, Publications Division, Ministry of Information and Broadcasting (India), Government of India. p. 1208. ISBN 978-81-230-1617-7.