Hadiza Sabuwa Balarabe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hadiza Sabuwa Balarabe
Deputy Governor of Kaduna State (en) Fassara

2015 -
Rayuwa
Haihuwa Sanga
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Matakin karatu Bachelor of Medicine, Bachelor of Surgery (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, spaceship's surgeon (en) Fassara, health professional (en) Fassara da uwa
Employers Jihar Kaduna
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Hadiza Sabuwa Balarabe Yar'Najeriya ce, yar'siyasa, wanda aka zaba tazama mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna, Najeriya. An kuma zaɓe ta tareda da gwamna maici wato Nasir Ahmad el-Rufai a watan February shekara ta dubu biyu da Sha Tara 2019, karkashin jam'iyar APC.[1][2][3][4]

A ranar 15 ga Oktoba, 2019, a matsayinta na gwamna, ta gabatar da kasafin kudin sabuwar shekara ta 2020 na gwamnatin jihar Kaduna a gaban majalisar dokokin jihar Kaduna, inda ta zama mace ta farko da ta taba yin hakan a Arewacin Najeriya.[5][6]

A shekarar 2022, ta yi burin tsayawa takarar gwamna a zaben 2023 amma ta janye, aka zabe ta a matsayin mataimakiyar dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani.[7][8][9]

A watan Maris na 2023, an sake zabar ta a matsayin mataimakiyar gwamna.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Balarabe haifaffen gidan Alhaji Abubakar Balarabe ne a karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna. Ta halarci makarantar ‘yan mata ta Soba don yin karatun sakandare, sannan ta samu admission a babbar Jami’ar Maiduguri inda ta yi karatun likitanci sannan ta kammala MBBS a 1986.[10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.