Jump to content

Halima Abdallah Bulembo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Halima Abdallah Bulembo
Member of the National Assembly of Tanzania (en) Fassara

29 Oktoba 2015 -
Election: 2015 Tanzanian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Kagera Region (en) Fassara, 1 ga Afirilu, 1991 (34 shekaru)
ƙasa Tanzaniya
Harshen uwa Harshen Swahili
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Swahili
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Halima Abdallah Bulembo (an Haife ta 1 ga watan Afrilu 1991) Hakimar Gundumar Muheza ce a yankin Tanga. Kafin naɗin nata, Halima Abdallah Bulembo ta kasance 'yar majalisar wakilai ta musamman a yankin Kagera a Tanzaniya. [1] An naɗa ta a kujerarta a watan Nuwamba 2015, inda ta zama 'yar majalisa mafi ƙarancin shekaru a majalisar dokoki ta 11 ta Tanzania kuma tana kan muƙamin har zuwa watan Oktoba, 2020. [2] [3]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Halima Abdallah Bulembo a watan Afrilu 1991 a Kagera, Arewa maso yammacin Tanzania. Ta shiga makarantar firamare ta Nyasho a shekarar 1998 kuma ta kammala a shekarar 2004. Daga nan ta shiga makarantar sakandiren Dr. Didas a shekarar 2005 kuma ta kammala matakin O a shekarar 2008. A cikin shekarar 2009, ta shiga makarantar sakandare ta St. Anne Marie Academy kuma ta kammala a shekarar 2011. Daga nan sai Halima ta yi karatun digiri na farko a jami’ar Tumaini a shekarar 2011, ta kammala a shekarar 2014. [1]

Rayuwar siyasa da gogewa

[gyara sashe | gyara masomin]

Halima ta fara aikinta na siyasa ne da farko a matsayin mai zawarcin jam’iyya mai mulki, Chama cha Mapinduzi (CCM) a shekarar 2002 yayin da kuma ta kasance mamba a kwamitin kula da harkokin Scout na ƙasa har zuwa shekara ta 2006. A wannan lokacin kuma ta kasance mamba a majalisar zartarwa ta Umoja wa Vijana wa CCM (UVCCM), reshen matasa na jam'iyya mai mulki.

An naɗa ta zama ‘yar majalisar wakilai ta musamman a shekarar 2015. Wa'adin ta ya ƙare a watan Oktoba 2020. [1]

  1. 1.0 1.1 1.2 "Parliament of Tanzania". www.parliament.go.tz. Archived from the original on 2016-12-08. Retrieved 2016-12-08.
  2. "Mbunge mwanamke mwenye umri mdogo Tanzania - BBC Swahili". BBC Swahili (in Harshen Suwahili). 23 November 2015. Retrieved 2016-12-08.
  3. Kamala, James (2020-06-17). "Tanzania: Youngest Legislator Speaks Out". allAfrica.com (in Turanci). Retrieved 2021-08-12.