Jump to content

Hamisu Breaker

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hamisu Sa'id Yusuf wanda aka fi sani da Hamisu Breaker kuma sunan na Breaker ya samo asaline a lokacin da yana yin wani salon rawa da ake kira breaking dance tun a baya kafin asan shi a matsayin mawaki. Shahararren mawakin hausa ne musamman wakokin soyayya wanda sunan sa ya shahara a Najeriya musammam ma yankin Arewa.[1]

Hamisu Breaker ya yi fice a tsakanin masu jin harshen Hausa a lardin Afirka ta Yamma, musamman a Arewacin Najeriya, Nijar, Kamaru, Cadi, Côte d'Ivoire da dai sauransu.

Rayuwar Farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Hamisu Breaker ne a shekarar alif dari Tara da casa'in da biyu 1992 a Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano Najeriya.

Hamisu Breaker ya halarci makarantar firamare da sakandare a Dorayi duk da har zuwa yau mawakin babu wani rahoto da yake nuni da ya cigaba da karatun jami'a.

Fara wakarsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Breaker ya fara Waka ne tun lokacin yana makarantar sakandare. Kuma ya yi wakoki da dama kafin ya fara ftar da album. Wakarsa da ta yi tashe sama da ko wacce ita ce Jaruma musamman a cikin Hausawa. A shekara ta 2020, Jaruma ita ce wakar Hausa ta soyayya da aka fi kallo da sauraro domin saida takai wani mataki a YouTube da babu wata wakar da ta taba kaiwa a kankanin lokaci a tarihin wakokin hausa. Domin yanzu haka an kalli wakar Jarumar Mata sau sama da miliyan goma a Youtube. Wasu daga cikin wakokinsa:

    • Jaruma
    • Muradin zuciya
    • so ne
    • Qanwa ta
    • Abincin Ruhi

Hamisu Breaker Latest Music Update Archived 2024-07-07 at the Wayback Machine