Hamza Al-Mustapha
Hamza Al-Mustapha (an haife shi a ranar 27 ga watan Yulin shekarar 1960) Manjo ne na sojan Najeriya mai ritaya, jami’in leken asiri kuma dan siyasa wanda ya rike mukamin babban jami’in tsaro ga shugaban kasa Janar Sani Abacha daga 1993 har zuwa rasuwarsa a ranar 8 ga watan Yunin shekarar 1998.
Rayuwar Farko
[gyara sashe | gyara masomin]Hamza Al-Mustapha haifaffen gidan Hausa ne kuma yayi karatu a Nguru. Ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya da ke Kaduna sannan ya shiga aikin sojan Najeriya a shekarar 1983
Aikin Soja
[gyara sashe | gyara masomin]Aikin soja Daga watan Agustan shekarar 1985 zuwa Agustan shekarar 1990, Al-Mustapha ya kasance Aide-de-camp (ADC) (amma kwanan nan ya fayyace a wata budaddiyar tattaunawa da gidan Talabijin na Channels Television Seun Okinbaloye cewa shi ba ADC bane cewa shine babban jami’in tsaro) ga babban hafsan sojin kasa, Janar Sani Abacha. Babban shugabansa da shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida, sun amince da iyawarsa, kuma sun ba shi iko na musamman, wanda ya zarce sauran hafsoshin da ke kan mukaminsa. Wannan ya kara nuna shi a matsayin mai karfi a matsayin soja.[1]