Jump to content

Harshen Kurame na Yahudawa na Aljeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harshen Kurame na Yahudawa na Aljeriya
sign language (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Aljeriya

Harshen Kurame na Yahudawa na ƙasar Aljeriya (AJSL), wanda aka fi sani da Harshen Kurame na Ghardaia, yaren kurame ne na ƙauye wanda ya samo asali ne daga Ghardaïa, Aljeriya wanda yanzu ake amfani dashi a Isra'ila kuma mai yiwuwa ma a Faransa.[1][2]

Al'ummar Yahudawa na Ghardaïa sun yi hijira zuwa Faransa da Isra'ila a cikin shekarun 1943 zuwa 1962. Koyaya, saboda Yahudawa kurame na Aljeriya sun auri Isra'ilawa kurame daga wasu asali, sun karɓi Harshen Kurame na Isra'ila (ISL) a matsayin yarensu na farko kuma AJSL yanzu ana amfani da ita ne kawai ga tsofaffi.[1]

Ba a san komai game da amfani da shi a Faransa ba.

Haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]