Hausa HipHop

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Hausa Hip Hop Ko Hausa rap dai za’a iya cewa wakar gambara ce ta zamani tinda dai duka dai zubo bayanai da malamai ne. Yawancin mawakan gambarar ta zamani sukan yi wakar ne cikin harshen Hausa da kuma turanci (Wato ingausa). An dade da fara shi a arewacin Najeriya. Mawaki Nomiis Gee shine data saga cikin fitattun mawakan da suka tallata harkar ta Hausa hip-hop ga duniya da shirin sa Wanda Arewa24 Duke haskawa wato Zafafa10 da HHiphop Wanda take gabatarwa da abokin aikin sa Ricqy Ultra. Kana daga baya sai aka samu Bullar wasu mawakan Hausa raps din daga Ghana (irin su Ghali Ghana, NT4, Labaran da kuma Mo Qid) Matasa da dama sun fara cin albarkar wannan sana’a, Abin birgewa da kuma ban sha’awa a cikin sana’ar shi ne babu hayaniyar wane ya fi wane kamar a sauran wurare, kusan a kowanne lokaci za ka ga yadda mawakan ke tallafawa juna ta hanyar tallata ayyukan sauran gami da girmamawa a shafukan sada zumunta ko kuma ta hanyar hadewa ayi maja waje guda ayi waka kamar yadda wata kungiyar mawakan Hausa rap din wato (YNS) sukayi ta haduwa waje guda sunayin wakoki masu dadi da suke Jan hankalin al’umma. Wadannan wakoki sun hada da YNS cyper 2019 (wanda su DJ AB da Jigsaw da Tee Swaggs da Lil Prince suka yi)sai kuma wakar “Da so samu ne” ( DJ AB da Jigsaw da Tee Swaggs da Feezy da Zayn Africa da Kibzy da kuma Deezell) sai wakar da Deezell yayi da wasu makan kungiyar su ta YNS mai taken “Duk abinda zai faru ya faru, daga karshe sai wakar Deezell Mai taken Girlfriend Wanda yayi da Mr 442 da Lsvee da Cdeeq da Boyskiddo da Tripple D da kuma Lil Prince

A ranar 14 ga watan Mayu ne dai kwatsam Morell ya saki maimaicin tsohuwar wakarsa mai taken “Ba Wani Bugatti” a shafin sa na Instagram inda ya yi aiki tare da Classiq, kuma a shafinsa na soundcloud, ya rubuta “This song supposed to drop last year so……” ma’ana “ya kamata a ce an saki wannan wakar a bara amma....”, a guje mabiyansa suka dinga garzayawa domin sauraro da sa ran cewa wakar za tayi wuta.🔥

Wannan ba shi ne karo na farko da gwarazan mawakan suka yi aiki tare ba, a’a sun yi wakoki da dama, daya daga cikin ayyukansu da aka so harma wakar da Deezell, ya gayyace su ciki mai taken “Babu Ruwan Mu Da Haterz” tare da wasu mawakan da nake kauna irin su DJ ABWanda shine Karon farko da mawakan gambarar hausa suka hadu waje guda sukayi waka.

Haka zalika daga baya bayan nan ma Many an shahararrun mawakan Hausa Hip Hip da sukayi fice kuma suka fi shahara DJ AB Kheengz Deezell da kumaBOC Madaki sun hadu waje guda sunyi Album Mai taken “Four Horsemen”. Wakokin cikin album din sune T4HM Cyper , Buro’uba , 240 , da kuma Real shit