Jump to content

Haven Coleman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Haven Coleman
Lua error a mw.lua, layi na 656: invalid value (nil) at index 1 in table for 'concat'.
Rayuwa
Haihuwa2006 (19/20 shekaru)
ƙasaTarayyar Amurka
Sana'a
Sana'aschoolchild (en) Fassara, environmentalist (en) Fassara da Malamin yanayi

Haven Coleman (an haife ta a ranar 29 ga watan Maris, shekara ta 2006)[1] 'yar ƙasar Amirka ce mai fafutukar hakkin yanayi da muhalli.[2] Tare da ita aka kafa kuma itama darekta ce na Yajin aikin Yanayi na Matasan Amurka tare da masu gwagwarmayar matasa Alexandria Villaseñor da Isra Hirsi.[3][4] Kungiya mai mayar da hankali kan wayar da kai da kuma kawo canji a kan matsalolin da ke janyo Canjin yanayi.[5]

Rayuwa ta farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Haven Coleman a Denver, Colorado.[1] Ita daliba ce a Makarantan Jama'a na Denver.[6]

Yunkurin fafutuka

[gyara sashe | gyara masomin]

Coleman ta fara jin sha'awar kare muhalli tun tana shekara goma: bayan ta koyi cewa dabbobin da ta fi so, wato sloths, suna raguwa saboda sare dazuzzuka. Daga nan ta yi babban sauyi a rayuwarta don rayuwa mai dorewa.[7] Horon da ta samu a Climate Reality Project ya kara mata ilimi sosai.[8]

Bayan ganin gwagwarmayar muhalli ta Greta Thunberg da yajin aikin yanayi na matasa a Turai, ta samu karfin gwiwan yin hakan. Don haka, tun daga watan Janairun 2019,[5] tana da shekaru 13, ta fara zanga-zanga a gaban kasuwanni ko gine-ginen gwamnati,[9] irin su Colorado State Capitol.[10] Kowace Jumma'a tana zuwa yajin aiki don neman matakin siyasa game da ingancin iska, ritaya daga masana'antar kwal, makamashi mai sabuntawa, da dai sauransu. Ta kuma aika da zaɓaɓɓun jami'ai game da batun. Abokan ta a makaranta sun tsananta mata sosai wadanda suka yi tunanin cewa gwagwarmayarta ba ta da kyau.[7]

Coleman ta yi zanga-zanga ita kadai har sai da ta sami damar kafa Yakin Yanayi na Matasan Amurka tare da Isra Hirsi da Alexandria Villasenor.[11] Tun daga wannan lokacin, an gudanar da yajin aikin yanayi a fadin jihohi da yawa a Amurka.[12] A ranar 15 ga watan Maris, an gudanar da zanga-zangar matasa ta kasa da kasa tare da kasashe sama da 120+ da ke da hannu.[13]

Coleman ta fara shahara bayan ta yi magana da Sanata Cory Gardner game da masu gurɓata carbon a wani taron jama'a a zauren gari. Ta roƙe shi ya dauki mataki kuma ya ba da gudummawa don shirya wani yunkuri don sauƙaƙewa, duk da haka, Gardner ya ki.[9]

Yayin da ta yi kanun labarai, ta ja hankalin Al Gore, wanda ya gayyaci Coleman don yin magana don kamfen ɗin 24 Hours of Reality wanda The Climate Reality Project ya shirya.

Coleman a halin yanzu tana aiki a Kukuma Arid Agency, wanda aka tsara don hanzarta kamfen ɗin muhalli da adalci na zamantakewa.[14]

  1. 1 2 Harmeet Kaur (March 15, 2019). "She's 12 and she's trying to save the world by skipping school". CNN. Cable News Network. Retrieved September 10, 2020.
  2. ↑ "Skipping School Around The World To Push For Action On Climate Change". NPR.org (in Turanci). March 14, 2019. Retrieved September 10, 2020.
  3. ↑ Nardino, Meredith. "Meet the 13-Year-Old Organizer of the US Youth Climate Strike". DoSomething.org (in Turanci). Retrieved September 10, 2020.
  4. ↑ "19 youth climate activists you should be following on social media". Earth Day (in Turanci). June 14, 2019. Retrieved September 10, 2020.
  5. 1 2 "Climate Reality Leader Haven Coleman Talks Today's Youth Climate Strike". Climate Reality (in Turanci). The Climate Reality Project. March 15, 2019. Retrieved September 10, 2020.
  6. ↑ Eastman, Katie (September 19, 2019). "A Denver teen goes on strike for the climate every Friday – and this week, she will march with Greta Thunberg in NYC". KUSA.com. Retrieved September 10, 2020.
  7. 1 2 Minutaglio, Rose (March 14, 2019). "The World Is Burning. These Girls Are Fighting to Save It". ELLE. Hearst Magazine Media, Inc. Retrieved September 10, 2020.
  8. ↑ Borunda, Alejandra (March 13, 2019). "These young activists are striking to save their planet from climate change". Environment (in Turanci). National Geographic Partners, LLC. Archived from the original on March 15, 2019. Retrieved September 10, 2020.
  9. 1 2 Kutz, Jessica (February 23, 2019). "Meet the 12-year-old activist taking politicians to task over climate change". Grist. Grist Magazine, Inc. Retrieved September 10, 2020.
  10. ↑ Budner, Ali (March 13, 2019). "Meet the Mountain West Teens Organizing the U.S. Youth Climate Strike". Elemental. Archived from the original on April 17, 2021. Retrieved September 10, 2020.
  11. ↑ Li, Ang (March 14, 2019). "'It Will Be Too Late for My Generation.' Meet the Young People Organizing a Massive Climate Change Protest". Time. Time Inc. Archived from the original on July 20, 2024. Retrieved September 10, 2020.
  12. ↑ Budner, Ali (March 12, 2019). "Meet The Mountain West Teens Organizing The US Youth Climate Strike". Colorado Public Radio (in Turanci). Retrieved September 10, 2020.
  13. ↑ Barclay, Eliza; Amaria, Kainaz (March 15, 2019). "Photos: kids in 123 countries went on strike to protect the climate". Vox (in Turanci). Vox Media, LLC. Retrieved September 10, 2020.
  14. ↑ "Haven Coleman". SXSW EDU 2020 Schedule (in Turanci). SXSW, LLC. Archived from the original on April 17, 2021. Retrieved September 10, 2020.