Heedayah (littafi)
| littafi | |
| Bayanai | |
| Kwanan wata | 2021 |
Heedayah littafi ne na Hausa da marubuciya Bilyn Abdull ta rubuta. Littafin ya shahara a fagen litattafan soyayya na zamani da ake wallafawa ta yanar gizo. An fara wallafa shi a shekarar 2021, kuma ya janyo hankalin matasa da dama.
Labari
[gyara sashe | gyara masomin]Labarin ya mayar da hankali ne kan wata yarinya mai suna Heedayah, wadda take da halaye na kamun kai da hankali. Littafin yana ɗauke da darussa masu yawa kan rayuwa, soyayya, da yadda mutum ke iya jurewa jarabawa da sauyin rayuwa. An cusa soyayya mai tsabta da tarbiyya a cikin labarin.[1]
Marubuciya
[gyara sashe | gyara masomin]Bilyn Abdull marubuciya ce da ta yi fice wajen rubuce-rubucen Hausa musamman a fannin soyayya da zamantakewa. Heedayah na ɗaya daga cikin fitattun littattafanta da suka shahara a dandalin Hausa Novels.[2]
Karɓuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Littafin ya samu karɓuwa sosai daga masu karatun Hausa.