Hilary Denise Arko-Dadzie
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Ghana |
Karatu | |
Makaranta |
Kwame Nkrumah University of Science and Technology University of East London (en) ![]() |
Matakin karatu |
Digiri MBA (mul) ![]() |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa |
Employers |
African Regional Intellectual Property Organization (en) ![]() |
Hilary Denise Arko-Dadzie ƙwararriya ce ta IT kuma masaniyar dabarun kasuwanci. Ita ce mace ta farko da aka naɗa a matsayin ma'aikaciyar gudanarwar hukumar kula da kadarorin yankin Afirka (ARIPO) da ke Harare, Zimbabwe. Haka kuma ita ce mace ta farko da aka naɗa a matsayin mambobi biyar na kwamitin zartarwa na ARIPO. [1] [2] [3] [4]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Arko-Dadzie ta halarci Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah, inda ta sami digiri na farko a fannin Kimiyyar na'ura mai kwakwalwa. Ta yi MBA a General Management daga Jami'ar Gabashin London a Burtaniya, da kuma takaddun shaida na IT da Gudanarwa daga Cisco, da Jami'ar George Washington. [1] [2] [3] [4]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]A halin yanzu Arko-Dadzie ita ce mace ta farko da ta zama shugabar aiyuka na kamfani na kungiyar kula da kadarorin yankin Afirka kuma mace ta farko da aka naɗa a matsayin mambobi biyar na kwamitin zartarwa na ARIPO. Kafin naɗin nata, ta yi aiki da Airtel, inda ta yi aiki a matsayin darakta na TowerCo na Airtel Ghana a yanzu Airtel Tigo da kuma mukaddashiyar shugabar Airtel Saliyo. Lokacin da ta shiga Airtel Ghana a shekarar 2009 a matsayin manajar ayyuka, ta kasance mai kula da manyan ayyuka kamar shigar da 3.75 G na Airtel Ghana, Mobile Number Portability da ƙirƙira da ƙaddamar da Airtel Premier. [1] [2] [3] [4]
Kyautattuka
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Ghana's international business leader Hilary Arko-Dadzie honoured". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2018-05-26. Retrieved 2019-11-03. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ 2.0 2.1 2.2 "Ghanaian business woman becomes first ARIPO executive member". www.pulse.com.gh (in Turanci). 2017-06-22. Retrieved 2019-11-03. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":1" defined multiple times with different content - ↑ 3.0 3.1 3.2 "Hilary Arko–Dadzie recognized for shinning the light for women in Zimbabwe". www.ghanaweb.com (in Turanci). Retrieved 2019-11-03. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":2" defined multiple times with different content - ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 "Ghana's Hilary Arko–Dadzie Recognised For Shinning The Light For Women In Zimbabwe". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2019-11-03. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":3" defined multiple times with different content - ↑ "Ghana's Hilary Arko-Dadzie Shines in Zimbabwe, Receives Prestigious Award". African Eye Report (in Turanci). 2018-05-24. Retrieved 2019-11-03.
- ↑ Davis, Eugene. "Hilary Arko-Dadzie recognised in Zimbabwe …for shining the light for women | Business & Financial Times Online" (in Turanci). Archived from the original on 2019-11-03. Retrieved 2019-11-03.