Jump to content

Himalaya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Himalaya
General information
Gu mafi tsayi Mount Everest (en) Fassara
Height above mean sea level (en) Fassara 8,848.86 m
Tsawo 2,400 km
Fadi 250 km
Yawan fili 600,000 km²
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 29°N 84°E / 29°N 84°E / 29; 84
Bangare na Alpide belt (en) Fassara
Larger Himalaya (en) Fassara
Kasa Nepal, Myanmar, Sin, Pakistan, Indiya, Afghanistan da Bhutan
Geology
Period (en) Fassara Eocene (en) Fassara
Taswirar tsaunukan Himalaya, yana nuna kasashen da ya ratsa.
Tuddan everest mafiya tsayi a tsaunukan Himalaya

Himalaya wani yankin tsaunuka ne dake a nahiyar Asiya. Karshen Himalaya daga yamma yana a kasar Pakistan. Tsaunukan sun shiga ne ta Jammu da Kashmir, Himachal Pradesh , Uttaranchal, Sikkim da Arunachal Pradesh a yankin Kasar Indiya, Nepal , da Bhutan. Karshen sa daga gabashi yaje har Tibet. Sun rabu zuwa yankuna 3 Himadri, Himachal da Shiwaliks. Tsaunuka 15 mafiya tsawo a duniya na a Himilaya. Daga ciki akwai tsaunukan Mount Everest, K2 , Annapurna, da Nanga Parbat . Mount Everest shine mafi tsawon tsauni a duniya da tsawon mita 8,849. Daga cikin dogayen tsaunuka mafiya tsayi a duniya Tara na a yankin Himalayan Nepal. Kalmar "Himalaya" na nufin gidan kankara da yaren Sanskrit, tsohon yaren Indiya. Tsaunukan Himalaya sune suka raba al'adun Sinawa da Indiyawa na tsawon lokaci. Da yaren Sanskrit, tsohon yaren Indiya. Tsaunukan Himalaya sune suka raba,wanda yagano himalayas a shekarar Alib1733,Shine wani masanin yanayin da yasha fa Duniya(Jean-Baptiste),Dan kasar francar ne,Save Open… Zoom image… 179x127 4.4 kB JPEG.

Gandun daji[gyara sashe | gyara masomin]

Jar Panda a Himalaya

Himalaya waje ne da yayi kaurin suna sosai a tsakankanin yan yawon bude ido da shakatawa sabo da albarkar yanayin da ke akwai na gandun daji. daga cikin tsirrai da bishiyoyin dake akwai sun hada da Oak, Pine, Fir, Rhododendron , Birch, Juniper,da Deodar. Ire iren dabbobin da ke akwai a sassan dazuzzukan Himalaya sun hada da damusa, Shidiyar Tinkiya, Giwa, Kada da Kura. A yankin kudancin Himalaya kinda akwai yanayin Sanyi sosai, dabbobi basu cika zama a wuraren ba. Haka kuna su wadanda ma keep rayuwa a wuraren, lokacin sanyi sukanyi hijira zuwa yankunan da sanyin ke da sauki. Wasu daga cikin guraren gandun daji masu jan hankali

  • Jim Corbett National Park
  • Namdhpha National Park
  • The Royal Chitwan Park
  • Kaziranga National Park
  • Royal Bardia National Park
  • Great Himalayan National Park
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]